Labaran chikin kasa Nigeria ::: wai Maine gaskia abinne Gwamnatin tarayya bata sakar mana N15.89bn da ake yayatawa ba - ASUU - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran chikin kasa Nigeria ::: wai Maine gaskia abinne Gwamnatin tarayya bata sakar mana N15.89bn da ake yayatawa ba - ASUU

<
Kungiyar malaman jami'o'i ASUU, ta ce bata da wata masaniya kan cewar gwamnatin tarayya ta sakarwa jami'o'i zunzurutun kudi har N15.89bn
- Wani rahoto da ake yadawanya bayyana cewa cewa gwamnati ta saki kudaden ne a ranar31 ga watan Disamba 2018 don biyan wasu basussukan albashi na malaman jami'o'in
- Sai dai shugaban kungiyar ASUU na kasa, Farfesa Biodun Ogunyem ya ce basu samu wata takarda daga gwamnati kan haka ba, amma zasu yi zama a ranar Litinin
Kungiyar malaman jami'o'i ASUU, ta ce bata da wata masaniya kan cewar gwamnatin tarayya ta sakarwa jami'o'i zunzurutun kudi har N15.89bn, watanni biyu bayan shiga yajin aikinta, kamar yadda taji ana yayatawa a kafafen watsa labarai.
Shugaban kungiyar na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi, ya bayyana hakan a zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a jihar Legas, a yammacin ranar Laraba..
Kungiyar na mayar da martani ne kan rahotannin da wasu kafofin watsa labarai da kuma na sadarwar zamani suke yadawa na cewar gwamnatin tarayya, a ranar 31 ga watan Disamba 2018, ta sakarwa jami'o'i N15.89bn.
Kanzon kurege: Gwamnatin tarayya bata sakar mana N15.89bn da ake yayatawa ba - ASUU
Kanzon kurege: Gwamnatin tarayya bata sakar mana N15.89bn da ake yayatawa ba - ASUU
Rahoton ya bayyana cewa an saki kudaden ne don biyan wasu basussukan albashi na malaman jami'o'in.
"Toh, wani ne ya jawo hankalina kan wannan rahoto. Ni ban karbi wata takarda a hukumance daga gwamnatin tarayya ba, mai dauke da wani bayani kan hakan. Sakon dana samu daga ministan watsa labarai a yammacin yau shine sun yi kokarin yin wani abu akan bukatarmu; me suka yanke ban sani ba.
"Sai dai kawai ya sanar da ni cewa akwai taron ganawa tsakanin mu (ASUU) da gwamnatin tarayya a ranar Litinin. Har sai munje wajen taron ne zamu iya sanin hakikanin matakin da gwamnatin ta dauka, idan ya yi mana to shi kenan, idan kuma bai mana ba, to zamu dauki maraki na gaba," a cewarsa.
Idan za a iya tunawa, a ranar 4 ga watan Nuwamba 2018, kungiyar ASUU tare da daukacin mambobinta dake fadin kasar, suka shiga yajin aiki, akan abun da suka bayyana a matsayin yajin aikin sai baba-ta-gani, sakamakon gazawar gwamnatin tarayya na cika alkawuran da ta daukar masu tun 2009 da kuma bijirewa yarjejeniyar 2017.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.