Labaran chikin kasa Nigeria ::: Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kai harin su Shekau a Maiduguri - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran chikin kasa Nigeria ::: Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kai harin su Shekau a Maiduguri

<
Rundunar sojojin Najeriya sun tabbatar da cewa wasu tsirarun 'yan ta'addan da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne sun kai hari a garuruwan dake zagaye da garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Wannan tabbacin dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar da mai magana da yawun rundunar Kanal Onyema Nwachukwu ya fitar inda ya bayyana cewa amma yanzu komai yana akan tsari domin suna kan shawo matsalar.
Yanzu-Yanzu: Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kai harin su Shekau a Maiduguri
KU KARANTA: An rufe gidajen karuwai a jihar Neja
Legit.ng Hausa ta samu cewa Kanal Onyema ya kara da shawartar al'umma mazauna yankunan da abun ya shafa da ma dukkan kasar da su cigaba da gudanar da rayuwar su kamar yadda suka saba su kuma kai rahoto ga jami'an tsaro idan suka ga bakuwar fuska.
Ya kara da cewa rundunar tana nan tana kokari ba dare ba rana wajen ganin ta kakkabe dukkan sauran 'yan ta'addan a duk inda suke.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.