Labaran chikin kasa Nigeria :: me duniya ina zaki damu ? - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran chikin kasa Nigeria :: me duniya ina zaki damu ?

<
An tsinci wani jinjiri kunshe cikin tsinma a daji a kauyen Giri da ke Gwagwalada a Abuja
- Wasu matasa ne da ke hanyarsu ta zuwa gona suka ji kukan jinjiri kuma suka bincika suka gano shi a cikin daji
- Sun koma kauyen sun sanar da mutane kuma daga bisani aka kai jinjirin gidan marayu na Gwagwalada
An tsinci jinjira da wata mata ta jefar a daji
An tsinci wani jinjiri da wata mata da ba san ko wacece ba ta jefar da shi a cikin daji a kauyen Giri da ke unguwar Gwagwalada na babban birnin tarayya, Abuja.
Daily Trust ta ruwaito cewa wata mata a kauyen na Giri mai suna Ramatu Danjuma ta ce wasu matasa ne da ke hanyarsu ta zuwa gona suka gano jinjirin kunshe cikin zani a safiyar ranar Talata.
Ta ce kukan jinjirin ne ye janyo hankulan matasan hakan yasa suka nemo inda ya ke sannan suka dawo kauyen suka sanar da mutane abinda suka gano.
DUBA WANNAN: Legas: An kama manyan 'yan kasuwa dake daukar nauyin 'yan bindigar Zamfara
" Ina tsamanin mahaifiyarsa ta jefar da jinjirin cikin dare ne. Wasu matasa da ke hanyarsu ta zuwa gona ne suka ji kukan jinjiri kuma bayan sun gano inda ya ke a cikin dajin suka dawo kauyen suka sanar da mutane," inji ta.
City News ta gano cewa daga bisani wata dattijuwa a kauyen da dauki jinjirin ta kai shi gidan marayu da ke Gwagwalada.
Anyi yunkurin tuntubar Kakakin 'yan sandan babban birnin tarayya, DSP Anjuguri Manzah domin ji ta bakinsa amma bai amsa wayarsa ba kuma bai amsa sakon kar ta kwana da aka aike masa ba.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.