Labaran chikin kasa Nigeria ::: Masu neman mulki a 2019 sun fara ajiye makami da kayan Sojojin bogi - Okereke - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran chikin kasa Nigeria ::: Masu neman mulki a 2019 sun fara ajiye makami da kayan Sojojin bogi - Okereke

<
Mun samu labari daga Jaridun gida cewa gwamnati ta gano cewa Gwamnoni da kuma wasu manyan ‘yan siyasa su na ta boye makamai da za a rabawa ‘yan iskan gari a babban zaben da za ayi kwanan nan.
An gano cewa sharrin da wasu ‘Yan siyasa ke kitsawa a kan zabe mai zuwa
Darekta Janar na hukumar da ke yaki da safarar manya da kananan makami a Najeriya, Dr. Osita Okereke ya bayyana cewa manyan ‘yan siyasan kasar nan sun fara dankare ko ina da mugayen makamai domin kawo hargitsi a zaben 2019.
Darektan hukumar ya fadawa ‘yan majalisar tarayya cewa akwai bukatar ayi maganin wannan abu. Sai dai Dr. Osita Okereke bai bayyana sunan ko guda daga cikin gwamnonin jihohi ko manyan ‘yan siyasan da ke kitsa wannan mugun aiki ba.
Okereke ya nemi Sanatocin Najeriya su amince da kudirin da zai haramta safarar manyan makamai da ma kananun cikin Najeriya, Okereke yake cewa akwai matukar bukatar a kauda makamai daga hannun bata-gari musamman kafin zaben 2019.
KU KARANTA: Jam'iyyar APC za ta hukunta Gwamnan ta da wasu mutanen sa
Darektan wannan hukuma yace ba a iya nan wadannan ‘yan siyasar su ka tsaya ba, domin kuwa a cewar sa, akwai wadanda su ka tanadi kayan sojoji da sauran jami’an tsaro da za a rabawa matasa domin su jefa kasar cikin hargitsi a lokacin zabe.
Akwai kudirin da ke gaban majalisa da ke neman a hana shigo da miyagun makamai cikin Najeriya wanda tun kwanaki aka nemi a kafa wannan doka amma har zabe ya karaso ba a iya yin hakan ba. A kwanan nan ne wa’adin da aka bada zai shude.
Idan an kafa wannan doka, ana sa rai cewa za a kawo karshen barnar da ake yi da bindigogi da sauran makamai a Najeriya. Gwamnati za ta dauki matasa aiki a fadin kasar domin tsare rayukan jama’a.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a:

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.