Labaran chikin kasa Nigeria ::: Dalilin da ya sa na maka CJN kotu - Tsohon kakakin Buhari - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran chikin kasa Nigeria ::: Dalilin da ya sa na maka CJN kotu - Tsohon kakakin Buhari

<
Mr Dennis Aghanya, ya karyata zargin cewa akwai hannun fadar shugaban kasa a karar da tawagarsa ta rubuta akan Mai shari'a Walter Onnoghen
- Ya ce tuni shi CJN ya amince da wannan zargi da ake yi masa a cikin takardar korafin
- Ya yi nuni da cewa kungiyarsa ta fara bincike kan badakalar da ake yiwa babban jami'in shari'ar tun shekara daya data gabata
Babban daraktan hukumar tattara bayanai kan binciken cin hanci da rashawa, Mr Dennis Aghanya, ya karyata zargin da ake yi na cewa akwai hannun fadar shugaban kasa a takardar korafin da tawagarsa ta rubuta akan babban joji na kasa, Mai shari'a Walter Onnoghen.
Da yake tsokaci kan masu zargin cewa korafin da suka shigar kan babban jojin kasar, cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari na da hannu a ciki, Aghanya ya shaidawa jaridar Punch, a daren ranar Asabar, cewar ko a 2011, ya maka Buhari kotu.
Ya ce tuni shi CJN ya amince da wannan zargi da ake yi masa a cikin takardar korafin.
KARANTA WANNAN : APC a Bauchi: Mun san munyi maka laifi, mun tuba ka yafe mana - Yuguda ya roki Buhari
Badakalar Onnoghen: Dalilin da ya sa na maka CJN kotu - Tsohon kakakin Buhari
Da yake zantawa da jaridar Punch ta ranar Lahadi a wayar talho, Aghanya ya ce, "Shin ko kunsan cewa na maka shugaban kasa kotu a 2011? Na taba rike mukamin hadiminsa amma na kaishi kotu.
"Wannan karace kungiya mai zaman kanta ta shigar. Shin ya za a ce kuma akwai sa hannun shugaban kasa? Mutane na son kaucewa ainin zancen ne kawai. Mu burinmu shine bayyana gaskiyar da aka boye. Bai kamata mutane su sanya siyasa a cikin lamarin ba."
Aghanya ya kara da cewa zai gudanar da taron manema labarai a wata rana da zai sanya don yiwa jama'a bayani kan lamarin. Haka zalika Aghanya ya ce kawo wannan batu ana daf da lokacin zabe ba zai canja komai ba.
Ya yi nuni da cewa kungiyarsa ta fara bincike kan badakalar da ake yiwa babban jami'in shari'ar tun shekara daya data gabata. Ya kuma ce ya zama wajibi a jinjinawa ARDI bisa bankado wannan badakala ta babban jojin kasar.
Abhanya ya ce ba gaskiya bane cewa sun shigar da karar wai don kawo rudani a fannin shari'ar kasar, ko kuma tallafawa shugaban kasa Muhammadu Buhari a yunkurin neman tazarcensa karo na biyu, yana mai cewa ya kamata mutane sufi mayar da hankali kan makomar shari'ar

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.