Labaran chikin kasa Nigeria ::: Atiku Abubakar ya wanke kan sa daga dukkan zargin rashawa lokacin yana jami'in kwastam - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran chikin kasa Nigeria ::: Atiku Abubakar ya wanke kan sa daga dukkan zargin rashawa lokacin yana jami'in kwastam

<
Dan takarar kujerar shugaban kasar Najeriya a karkashin tutar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar ya wanke kan sa daga dukkan zarge-zargen da ake yi masa na aikata ba daidai ba lokacin yana jami'in kwastam a shekarun baya.
Dan takarar yayi wannan bayanin ne lokacin da yake ansa tambayoyi daga 'yar jarida Kadaria Ahmad a wani shiri kain tsaye da dan takarar da mataimakin sa Peter Obi kan manufofin su.
Atiku Abubakar ya wanke kan sa daga dukkan zargin rashawa lokacin yana jami'in kwastam
KU KARANTA: Mumbarin kamfe ya rufta da dan takarar PDP a Kebbi
Haka ma dan takarar shugabancin kasar Najeriya a jam'iyyar adawa ta PDP, Alhaji Atiku Abubakar yace yana tunanin watakila idan ya lashe zaben da za'a gudanar nan da 'yan kwanaki zai yafewa dukkan wadanda suka taba sace dukiyar kasar nan.
Atiku Abubakar din ya bayyana cewa zai yafe masu ne a bisa sharadin cewa za su maido dukkan abunda suka sata sannan kuma su zuba su a cikin kasar Najeriya domin habaka tattalin arzikin kasar.
Haka zalika a wata tambayar da aka yi masa, Alhaji Atiku Abubakar ya ce karyace tsagwaron gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke shirgawa na cewa kasar na ta saida gangar danyen mai $100 a shekara 16 da suka yi suna mulki.
Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa maganar gaskiya Shugaba Goodluck Jonathan ce kadai ta saida danyen man a wannan farashin a kuma dan wani lokacin da yayi yana mulki na shekaru biyu kacal.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.