Labaran chikin kasa Nigeria ::: ASUU tayi watsi da tayin gwamnati, yajin aiki zai cigaba - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran chikin kasa Nigeria ::: ASUU tayi watsi da tayin gwamnati, yajin aiki zai cigaba

<
Kungiyar ASUU ta ce mambobinta ba su amince da tayin da gwamnatin tarayya tayi musu ba a yanzu
- Kungiyar ta dage kan cewa sai gwamnatin ta cika alkawurran da ke cikin yarjejeniyar da aka rattaba hannu tun a baya
- Gwamnatin tarayya ta bawa kungiyar N15.4 biliyan a matsayin kudin allawus sannan tayi alkawarin za ta saki wasu kudaden
Daliban jami'o'in Najeriya sun karayya a kan batun komawa makarantunsu a cikin 'yan kwanakin nan sakamakon kin amincewa da kungiyar ASUU tayi da tayin da gwamnatin tarayya tayi mata a farkon wannan makon.
A taron da su kayi a ranar Talata, Ministan Kwadago da Ayyuka, Chris Ngige ya ce ana gab da yin sulhu tsakanin ASUU da kungiyar Kwadago a yayin da ya lissafo sabbin alkawurran da gwamnati tayi wa kungiyar malaman.
Da duminsa: ASUU tayi watsi da tayin da gwamnati, yajin aiki zai cigaba
A cewar Ngige, ofishin babban akawu na Kasa da Ma'aikatan Kudi sun nuna wa ASUU shaidar cewa an amince da bawa jami'o'in Najeriya N15.4 biliyan.
DUBA WANNAN: 'Yan majalisar dokoki 2 sun fita daga APC a Jigawa
Ya kuma ce Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da biyan malaman N20 biliyan a matsayin allawus dinsu daga shekarar 2009 zuwa 2012.
Amma a wata hira na musamman da Premium Times tayi da shugaban ASUU, Biodun Ogunyemi a safiyar yau, ya ce mambobin kungiyar daga jami'o'i da dama sun ki amincewa da tayin na gwamnati.
Ya ce 'yan kungiyar suna dage a kan bakarsu na cewa gwamnati su biya wani kaso cikin N220 biliyan da za a kammala biya cikin shekarar 2019.
Ya kuma ce batun allawus din malaman, ba za su amince da wani kaso da ya yi kasa da adadin da gwamnatin ta biya a baya ba na N22.9 biliyan.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.