Labaran chikin kasa :: an bada Berlin Dino melaye abisa wasu sharadda - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran chikin kasa :: an bada Berlin Dino melaye abisa wasu sharadda

<
Kotu ta bayar da belin Dino Melaye bayan ya kwashe kwanaki a hannun 'yan sanda
- Sai dai kotun ta bukaci ya gabatar da mutane 3 da za su karbi belinsa kuma ciki har da magatardar majalisar tarayya
- Kotun ta bayar da belin sanatan ne domin ya samu cikaken kulawa daga likitocinsa kafin a gurfanar dashi
Wata babban kotu da ke Maitama a babban birnin tarayya Abuja ta bayar da belin Sanata Dino Melaye da halin yanzu ya ke tsare a asibitin rundunar 'yan sanda da ke Abuja.
Da duminsa: Kotu ta bayar da belin Dino Melaye
Alkalin kotun, Justice Yusuf Halilu ya bayar da belin saboda dalilan rashin lafiyar da sanatan ya ke fama dashi kamar yadda lauyan Dino Melaye, Mike Ozekhome ya shaidawa kotun a takardan neman belin.
Alkalin yana ganin Dino Melaye ba zai iya fuskantar shari'a ba idan bashi da lafiya kamar yadda The Nation ta ruwaito.
DUBA WANNAN: Sabon IG ya bayyana babbar matsalar da aikin dan sanda ke fuskanta a Najeriya
Ya ce tunda ba za a iya gurfanar da sanatan a kan gadon asibitin ba ya dace a bashi beli domin ya samu ya murmure.
Alkalin ya bukaci sanatan ya gabatar da mutane uku da za su karba belinsa, daya daga cikinsu kuma ya kasance magatakardan majalisar tarayya wadda zaiyi alkawarin gabatar da shi a kotu a duk lokacin da ake neman shi a nan gaba.
Ya ce sauran mutane biyun da za su karba belinsa kuma su kasance sun mallaki filaye ko gidaje a Abuja.
Ku biyo mu domin karin bayani ...

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.