Labaran afirka ::: An Rusa Daruruwan Gine-Gine A Birnin Accra - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran afirka ::: An Rusa Daruruwan Gine-Gine A Birnin Accra

<
Da sanyin safiyan Litini aka soma wani atisayin rusa daruruwan gine gine dake kurkusa da layin dogon Accra zuwa Tema domin kare layin dogon daga hadura
An soma atisayin ne daga titin da ake kira Graphic Road, ya ratsa Kwame Nkrumah Circle zuwa Avenue da Tesano, zuwa Harbour city tema.
A lokacin da Sashen Hausa ya ziyarci wurin ya tarar mazauna wuraren suna ta kokarin tattara inasu-inasu yayin da ake rurrusa matsugunan nasu. Wadansu da wakilin Muryar Amurka ya yi hira da su, sun bayyana cewa ba a sanar da su kakfin fara wannan aikin ba, yayinda wadansu kuma suka yi kira ga gwamnati ta samar masu da sabon matsuguni.
Daya daga cikin wadanda aka yi hira da shi ya bayyana cewa, ya kama daki a wannan wurin ne sabili da yana da saukin kudi idan aka kwatanta da sauran wurare.
A nasu bangaren hukumomin kanfanin jiragen kasar sun bayyana cewa, sun ba mazauna wadannan wurare isasshen lokaci su tashi daga unguwannin, amma suka yi watsi da gargadin.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.