Kannywood entertainment ::: Maine dalilin jamila umar nagudu naki auren mai kudi ? - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Kannywood entertainment ::: Maine dalilin jamila umar nagudu naki auren mai kudi ?

<
Fitaciyyar jaruar Hausa Jamila Umar Nagudu, ta bayar da dalilan da yasa bata son auran namiji mai kudi
- Jamila babban dalilin da yasa bata son auran mai kudi shine saboda ba zai samu dama da lokacin tattali da tarairayarta ba
- Hazalika tace bata burin auran miji talaka, kawai dai ya kasance mai rufin asiri
Jarumar dandalin shirya fina-finan Hausa na Kannywood, Jamila Umar Nagudu, ta bayar da dalilan da yasa bata son auran namiji mai kudi.
Jamila a wani shiri na Kannyflix ‘Mujallar Tauraruwa’ tace babban dalilin da yasa bata son auran mai kudi shine saboda ba zai samu dama da lokacin tattali da tarairayarta ba.
Kannywood: Dalilin da yasa bana son auran mai kudi – Jamila Nagudu
Kan irin mijin da take son aure tace “Bana son auran miji mai arziki, haka kuma bana son auran miji talaka”.
“Ina so na auri mutum da zai dauki nauyin bukatuna ciki harda samun lokain zama tare dani. Bana son miji mai tarin dukiya da yawa saboda yawan harkokinsa ba zai bari ya samu lokaci na ba, " inji ta.
Jamila ta fito a fina finai da dama kamar irin su Miji Da Mata, Wani Gari da kuma Jamila Da Jamilu.
KU KARANTA KUMA: Sababbin fina-finan Hausa na sabuwar shekarar 2019
A halin da ake ciki, mun samu labarin cewa Allah ya yiwa Shahararren ɗan wasan Hausa na Kannywood Sani Garba S.K rasuwa. Marigayin ya rasu ne bayan yayi fama da doguwar rashin lafiya.
Mun samu labarin rasuwar nasa ne a shafin Jaridar Dimokuradiyya.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.