Business ::: Aliko Dangote ya lashe kyauta mafi girma a fannin albarkatun man fetur - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Business ::: Aliko Dangote ya lashe kyauta mafi girma a fannin albarkatun man fetur

<
Alhaji Aliko Dangote dake zaman shugaban rukunin kamfanonin Dangote ya karbi kyauta mafi girma a fannin albarkatun man fetur ta Brevity Anderson akan gudummuwar da yake bayarwa wajen cigaban harkokin masana'antar musamman a Najeriya.
Majiyar mu ta kamfanin dillacin labaru ta ruwaito cewa da aka kira sunan hamshakin mai kudin dan asalin jihar Kano a Arewacin Najeriya, al'ummar dakin taron sun yi ta shewa da jin sunan sa a matsayin wanda ya lashe kyautar a taron bayar da kyaututtuna karo na biyu.
Namu-ya-samu: Aliko Dangote ya lashe kyauta mafi girma a fannin albarkatun man fetur
KU KARANTA: PDP ta yiwa Buhari dariya kan tara tsirarun mutane wajen kamfe a Imo
Legit.ng Hausa ta samu cewa taron wanda ya gudana a garin Abuja, Dangote ya samu wakilci ne daga shugaban tsare-tsare da dangantaka da gwamnati da sauran masu zuba jari na kamfanin Mista Ahmed Mansur.
Da yake karbar kyautar daga hannun ministan albarkatun mai na Najeriya Ibe Kachikwu, Dangote ya bayyana jin dadin sa sannan kuma ya yi alkawarin kara kaimi wajen cigaba da zuba kudaden sa domin habaka harkar ta ma'adanan man fetur a Najeriya da ma Nahiyar Afrika baki daya.
A wani labarin kuma, Dan takarar shugabancin kasar Najeriya a jam'iyyar adawa ta PDP, Alhaji Atiku Abubakar yace yana tunanin watakila idan ya lashe zaben da za'a gudanar nan da 'yan kwanaki zai yafewa dukkan wadanda suka taba sace dukiyar kasar nan.
Atiku Abubakar din ya bayyana cewa zai yafe masu ne a bisa sharadin cewa za su maido dukkan abunda suka sata sannan kuma su zuba su a cikin kasar Najeriya domin habaka tattalin arzikin kasar.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.