Najeriya::: Boko Haram ta kai hari kauyen Maiborti - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Najeriya::: Boko Haram ta kai hari kauyen Maiborti

<
Kungiyar Boko Haram ta kai hari kauyen Maiborti da ke wajen
Maiduguri, babban birnin jihar Borno da ke arewa maso
gabashin Najeriya.
Mayakan na Boko Haram sun kuma kona gidaje tare da
tursasawa mazauna kauyen tserewa daga muhallansu.
Ba bu dai tabbacin a kan ko an rasa rai ko rauni a yayin harin
da aka kai a kauyen.

Rundunar sojin kasar dai ta ce, ta mayar da martani a harin
inda sojojinta na kasa da na sama suka fatattaki mayakan na
Boko Haram daga kauyen.
Wannan dai shi ne hari na baya-bayan nan da kungiyar ta Boko
Haram ta kai a jihar ta Borno.
Rashin tsaro dai shi ne babban batun da ke kan gaba a taron
yankunan kasashen da ke makwabtaka da Najeriya da aka
gudanar a Abuja, babban birnin kasar.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.