Najeriya ::::: Atiku ya taya Buhari murnar zagayowar ranar haihuwa - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Najeriya ::::: Atiku ya taya Buhari murnar zagayowar ranar haihuwa

<
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya taya
Shugaba Muhammadu Buhari murnar zagayowar ranar
haihuwarsa.


Shugaban na Najeriya ya cika shekara 76 da haihuwa ranar
Litinin 17 ga watan Nuwambar bana.
A sakon da ya wallaf aa shafinsa na Tiwita, Atiku Abubakar ya
ce yana taya shugaban kasar murnar zagayowar ranar
haihuwarsa.


"Ina taya Shugaba @MBuhari murnar zagayowar ranar
haihuwarsa, kuma ni da iyalina muna masa addu'ar tsawon
rai."


Ya kara da cewa: "Duk da cewa ni da shi za mu hadu a fagen
zabe nan ba da jimawa ba, ina son tabbatar da cewa ni da shi
'yan uwan juna ne da kasarmu Najeriya ta haifa."

    I wish President @MBuhari a happy birthday even as my
family and I pray for long life for him. Despite the fact
that we will meet at the polls soon, I very much affirm
that we are brothers born from the womb of One
Nigeria. Happy birthday. -AA
— Atiku Abubakar (@atiku) 17 Disamba, 2018

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.