musha dariya :::: "abun mamaki da nishadi" - BESTAREWA BlOG

Header Ads

musha dariya :::: "abun mamaki da nishadi"

<
Wani danfulani ne ya shiga mota LUxurious daga Aba zuwa Yola,,,,,suna cikin tafiya motar ta kwace,,,mutanen ciki sai kiran JESUS sukeyi, danfulani ma yanata kiran JESUS! Da motar ta dawo daidai sai wata mata Igbo tace "meyasa baka kira Allanka bab kake kiran JESUS?". Sai danfulani yace "shegiya shashasha aini na zata JESUS sunan direban motar NE......

Mamana ce ta aikeni Bank domin sakawa yayana kudin Makaranta koda na Isa harabar Bank sai naga mutane akan layi sunata mika wata Takarda Ana basu kudi! Banyi kasa a gwiwa ba sai Natambayi wani malami cewar Inason turama yayana kudine Amman bansan yadda akeyiba! Sai mutumin yakarbi kudin yace jeka Dauko Tela a nuna maka yadda akeyi. Sai nace to Nagode kawai saina fito Nahau Mashin dina banyi burki ko Inaba sai shagon Telan Unguwarmu nace don Allah yazo muje Bank zaidan yimani wani aiki! Tela yadauko Tape rule dinsa muka koma Bank Da Isarmu sai Naga mutumin nan yanata fada kai daga ka miko Tela sai kaje kayi zamanka sai Nace ai gashi tare muke kasan Unguwar mu da dan tazara ai sai Naga kowa yakwashe da Dariya! Meye abun dariya?

A wata kotu dake Wudil ne wata mata ta kai karar mijinta kotu inda take zarginsa da cewar bai iya yanka lemo ba.

A ranar da aka gabatar da kara a kotu:

*Alkali ga wanda akayi kara*:

Matarka tana zarginka da cewa ba ka iya yanka lemo ba.

*Wanda akayi kara:* Cikin mamaki yace; Allah ya gafarta Mallam tayaya za'a dubi mutum kamata ace wai ban iya yanka lemo ba, anan ya bukaci da a kawo lemo ya yanka.  Alkali yasa aka kawo lemo da wuka aka bashi, sai ya yanka kuwa. Alkali ya dubi Matar yace; Malama kince bai iya ba, gashi ya yanka.

Sai Matar tace Allah ya gafarta Mallam akawo min na yanka a gani, za'a san bai iyaba;   Alkali yasa aka bata lemon da wuka. Da aka bata sai ta kama lugugutawa tana lallatsa lemon, har sai da yayi ruwa sosai, sa'ilin nan ta sanya wuka ta yanka, ai tana yankawa sai ruwa yana ta zuba shaaaaaa!! Sai ta kalli Alkali tace Allah ya gafarta Mallam wanene yafi iyawa? Alkali yace haka ne, gaskiya mijinki bai iya yanka lemo ba to amma na bashi biko ki je ki koya masa, sai Alkali kuma ya kalli wanda akayi kara, to, kaga yadda ake yanka lemo kuma kayarda cewa kai baka iyaba, saboda haka ka koma gida ka baiwa lemo hakinsa sosai!!!

Wata mata ce taji labarin mijinta zai yo mata kishiya don haka sai ta kira wata qawarta wadda take bazawarace tace ta bata shawara. Sai qawar tace wa matar ai idan mijin nata ya shigo gida toh ta kulle gidan sannan ta dauki wuqa tace ya saketa saki daya ko ta kasheshi kowacce ta rasashi. Sai qawar taci gaba da cewa bayan ya sakeki sai ki nemi wacece amaryar da zai auro sai kice mata yana da ta6in hankaline shi yisa kika gudu kika barshi don itama ta kiyaye kanta kar ta aureshi, toh bayan ta fasa sai ki dawo dakinki muje wajen wani boka ki mallake kayanki ke kadai. Sai sukayi shewa suka tafa sannan qawar ta kama hanya ta koma gida , ai fitarta keda wuya sai mijin waccan ya dawo ya kishingida don ya huta ya gaji. Kwatsam sai matar ta dauko wani ajiyayyen takobin mijin bama wuqa ba ta daga sama kamar zata datse masa kai sannan tace ya saketa saki daya ta tafi.

Toh shi kuma da yaga haka ya dauka ta haukace ne bayan gashi daman chan bata da tarbiyya don bata masa biyayya da tarairaya irin na aure mai dadi don haka da budan bakinsa sai yace ya saketa saki uku kenan yayi mata saki daya harda gyaran saki biyu sun zama uku sannan ya dauko biro da takarda ya tabbatar mata da sakin a rubuce. Sai ihu matar nan ta rikice ta ruga da gudu gidan qawarta bazawaran ta shaida mata tace tazo neman mafita ne a gurinta. Kunga da bazawaran nan ta kece da dariya har sai da qwalla ya fito mata a idanu sannan tace yayi mun kyau yayi dai kinga gida ya zama nawa ni kadai kenan don nice amaryar da za a auro maki shi yisa nayi maki qisisinarmu na mata don in koraki in gaje mijinki tunda ke baki iya tarairayarsa ba, so yanzu shawarata daya gareki qawata kije ki gama idda ki dan sha zawarci kema kiji sannan ki sami wani akwalan bazawarin da yayi kwantai ko kuwa kema kije kiyi wa wata qwace tunda na koya maki yadda akeyi, ko?

SAURAYI_DAN_GANGANCI
Wani saurayi ne yaje wajen budurwar sa hira. suna cikin hirar sai NEPA suka kawo wuta. sai ya tambaye ta yace yanaga ko,ina da wuta amma banda gidan ku? sai tace wlh lokacin ana ruwan sama shine iska ta tsinke WAYAR. sai yace to meyasa baku kira YAN NEPA sun gyara ba? sai tace, wlh mun kira su sunce zasu zo gashi yau har kwana 2 shuru. sai yace bakomai, abinda za,ayi shiga gida kisa YARA SU FITOMIN DA TSANI DA KUMA FILAYA. sai tace haba kawai ka barshi za,a gyara, SWEET HEART kaga ba aikin ka bane. sai yace haba MY LOVELY ai abun duk bigene. aka fitomai da TSANI DA SAURAN KAYAN AIKI ya hau FALWAYA ya fara aiki. can zuwa wani dan lokaci sai budurwar sa taji yayi wani MUGUN IHU HADE DA KARA wuta ta jahi ya fado cikin KWATA A SUME. bayan ya farfado daga suman da yayi, ya tashi zaune yana daga kansa sai yaga budurwar sa da baban ta da babarta da yaran gidan gaba 1 da kuma sauran yaran unguwar suna mai sannu. can saiji yayi wata karamar yarinya kanwar budurwar sa tace, LA, AUNTY SAURAYIN KI YAYI KASHI A WANDO. HHHHHHH.....

DAN SHAKATA
Wata Hajiya ta kira wasu gayu, 'yan shaye -shaye, don su gyara mata Ragon Layya.
Da suka gama aiki, sai ta zo dubawa, sai ta ga ba kayan ciki ko daya:
Sai ta ce masu, ina kayan cikin?
Sai dayan ya ce ma dayan: Yi mata bayani mana!
Sai dayan ya ce: Wallahi Hajiya, mu kanmu abin ya daure mana kai, domin kuwa, sai da muka bude cikin ragon, sai muka ga ashe ragon naki Tubeless ne

WASA KWAKWALWA
Misali, kai ne budurwarka ba ta da lafiya kuma ba zata warke ba har sai anje wani gidan gona an tsinko wani lemo, kuma shi ka'idar gidan gonan da lemo daya zaka iya fita, sannan a gidan gonan akwai kofofi guda 5, kuma kowace kofa akwai mai gadinta, haka sannan duk kofar da kaje sai ka raba lemon daka tsinko gida 2 ka bawa mai gadin kofar kaso 1 daga ciki, kuma gashi da lemo 1 ake so ka fita..... Wai shin lemo nawa ya kamata ka tsinko idan ka shiga ta yadda duk kofar da kaje koda ka raba gida 2 za ka samu damar fita da guda dayan daga karshe? ...Amsa ba mai wahala ba ce, amma sai an sha lissafi.

MATAR WANI.....
Wani gwanin iya magana ya ce : "Kwanaki mafi dadin dadadawa na rayuwa ta sune kwanakin da na yi da matar wani". Mahalarta taron suka yi shiru cike da mamaki. Sai ya kara da cewa: "ita ce Mahaifiya ta". Taro ya kaure da ihu da kuma tafi. Wani da ya halarci taron sai ya kudiri aniyar yi wa matarsa wannan barkwanci a gida. Bayan sun kammala cin abinci, sai ya ce da matarsa: Kwanaki mafi dadin dadadawa na rayuwa ta sune kwanakin da na yi da matar wani...... Bayan wani lokaci ya fara kokarin tuno ci gaban maganar...... Lokacin da ya dawo hayyacin sa, sai ya samu kansa kwance bisa gadon asibiti, ya na jinyar mummunar kunan da ya samu sakamakon Zazzafan kishi da ya kwashi matarsa ta kwarara masa tafasashen ruwan zafi. DARASI: Kasance Mai Kirkira Ba Mai Kwaikwaya Ba.

Musha dariya ...akwai wani likitn mahaukane,,,yana duba marasa lpy...sai yazo kan wani mahaukaci...yan
a shirin dubashi...kawai sai mahaukacin yazare wata doguwar wuqa..yabiyoshi
...likitan yanagudu..yana neman temako...amma dik fadin asibitin anrasa metemakonsa...har ya kawo..inda ba wurin gudu...kawai seya rufe ido...yanajira yaji saukan wuka akanshi....kawai seyaji mahaukacin...ya tintsire da dariya yamikamishi wukar yace ansa kaima kabiyoni...
...idan kaine ko kece yazakiyi???

Wani Sarki Ne Ya Tara Waziransa Guda Uku, Ya Basu Buhu Yace: "Kowanne Ya Tafi Gidan Gona Ya
Samo Mini Kayan Marmari"
Wazirai Suka Tafi.
* NA FARKO: Ya Ce:"Ai Da Alama Sarkina Yana Son Ya Ci Ne, Saboda Haka Ya Dukufa Da Nemo Kayan Marmari Masu Kyau".
* NA BIYU: Ya Ce:"Ai Sarki Ba Wani Tsayawa Zai Yi Yana Kula Ba, Saboda Haka Bari Na Kwaso Masa Masu Kyau Da Marasa Kyau Da Danyu".
* NA UKU: Kuma Ya Ce:"Ai Kawai Sarki Bama Zai Duba Ba, Saboda Haka Bari Kawai Na Kwaso Ganyaye, Da Shara Na Cika Buhu".
.
Kwatsam!
Suna Dawowa Sai Sarki Yasa a Kai Su Kurkuku, Kada a Bawa Kowa Abinci Kowa Ya Ci Abinda Ya Kwaso Har Tsawon Wata Daya.
.
• To Anan Fa Waziri Na FARKO Yayi Ta Cin Kayan Marmarinsa Lafia Lau.
• Na BIYU Kuwa Yayi Nadama Saboda Ya Hado Da Marasa Kyau.
• NA UKU Kuwa Yaita Cin Shara Da Ganyen Da Yabo Har Ya Mutu.

TSOKACI: "Ku sanya a ranku cewa kune aka sa awannan kukurku (KABARI) kun ga duk abinda kuka
tsinko na Alkhairi ko Sharri a duniya shi xaku gani, Sabi da haka, Yan uwana masu daraja mu dage wajen kwaso
abubuwan alheri, domin samin sakamako mai kyau."Allah yabamu sa'ah!Amiiin!!

INA NEMAN SANI!!!
Wani yaro ne yaje kasuwa sai yaga riga ta birgeshi yanaso amma kuma baida kudi saiya tambayi kudinta akace masa naira 100 sai yaje wajen mamarsa ya aro naira 50 kuma yaje wajen babansa ya aro naira 50, bayan yaje kasuwar saime rigar yarage masa naira 3 saiya tafi gida yamaida ma mamarsa naira 1 kuma ya maidama babansa naira 1 sai shikuma yaron yarike naira 1, to yanzu babanshi yana binshi naira 49 mamarshi ma tana binshi naira 49 idan aka tara bashin babanshi dana mamarshi 49+49=98 sai ahada da naira 1 dayake a hannun yaron sunzama 99, Abin tambaya anan ina ragowar naira 1 tashige?

KAI SAMARI AI AURE

 Yau ba aiki inah gida inah hutawa matata tana hada mun wani kayataccen kunun ayah da lemo mai dadi nikuma Na bararraje akan gado inah jiranta ta kawo min Bayan kamar minti daya sai gatanan dauke jug cike da kunun ayah tun kafin ta karaso yawuna ya tsinke Na mika hannu da niyar ta bani kawai sai taimun fari da ido Tace sweat hart bude bakin ka Na baka haka Na bude baki kamar wani karamin yaro tana tsiyaya mun inah tasha.... Kawai sai naji ana yayah ka tashi akuyar indo tanama fitsari abakiiiiiiiiiiiiii WAI ASHE MAFARKI NAKE WAYYO ALLAH

Wani gidan mahaukata ne aka lura da wasu mahaukata su uku kamar sun samu sauqi,bisa yadda suka kame kansu,sai wani daga cikin ma'aikatan gidan yace yakamata a sallamesu bayan an jarabasu,sai wani daga cikin ma'aikatan yasamo alli yazana hoton qofa ajikin bango,sai aka fito dasu akace tunda kunsamu sauqi ga qofa nan kufita an sallameku,sai biyu daga ciki suka ruga inda kofar take sunata kokawa wai sai sunfita,guda kuma na gefe yana kallonsu, sai ma'aikatan sukace wadancan basu samu sauki ba,wannan ne kawai yasamu sauki bari mutambayeshi don mu tantance, sai suka ce masa kai yaka tsaya ko bazaka fita bane?sai yace barsu mahaukata ne basusan mukullin qofar yana hannu na ba sai sun gama zan bude in fita.

Wata rana Shehu ya je kasuwa, sai ya hadu da wani mutum shi kuma ya siyo tangaram cike da buhu, sai ya ce ma Shehu, ka daukar man kayannan nawa
ka kaiman gida, ni kuma zan sanar dakai wasu abubuwa guda ukku da za su amfaneka har karshen rayuwarka, Shehu ya ce ya yarda,suna cikin tafiya har sun yi kashi daya cikin ukku na tafiyarsu, sai Shehu ya ce ka fada min yanzu, sai mutumin ya ce, na daya duk wanda ya ce maka da koshi gara yunwa karka gaskatashi Shehu ya ce to na biyu fa? Sai ya ce duk wanda ya ce maka da tafiya kan abin hawa gara tafiya a qasa karka gaskatashi, bayan sun isa kofar gidan mutumin sai Shehu ya ce ka fada min gudan sai ya ce duk wanda ya ce zan biyaka ladan daukar kayan nan karka gaskata shi, sai Shehu ya daga buhun tangaram ya rabkashi da kasa, sai ya ce duk wanda ya ce akwai sauran
tangaram mai rai a cikin buhunnan karkashin gaskatashi!

MUSHA DARIYA TSOHUWA DA DAN ACABA!!!!
Wata tsohuwace tahau mashindin wanidan achaba zaikaita unguwa inda zaikaita naira arbainne ake kaiwa tace yataimaka naira ashirin gareta yace tahau bakomi ketsohuwa dakika hau mashin kikaji anata tsula wuta dake saitarasa inda zata rike dan karta fado kawai taji wasu marikai guda biyu dagakasa ashe siginonine tsohuwarnanko tarikesu gamgam datajianshiga gargada garam!Garam! Saita kara makalkale siginoninnan daga karshedaikamin akaita inda zata sauka dukta kakkarya siginonin mashindinnan saidadan achabarnan yakaita bayantabashi ashirindin saita mika mishi siginonin tace karbi yaro abubuwan rikewar taka basuda kwari!!!Dan achabarnan yayi shiru yanakallon tsohuwarnan yarasa abinda zaiyimata yahuce karshe yace todan allah iya taimaka kirikeminsu muje wajan memashindin karya ce dagangannakaryasu saikiyimasa bayanitsohuwa tace bakomi da yadauketa yayita zuba gudu saida yayi tafiyarda ko naira darida hamsin bazata maida tsohuwarnanba kana ya tsaya yaceta sauka bayan tasauka yakalleta yace yarbanza kudin siginata yaja mashindinshi yatafi yabar tsohuwanan tsohuwa tafashe dakuka tace allah yaisa yaro kwarankwatsa naira goma taragemin!!!
Dan Allah wannan dan acaban wani gari da mukunta haka nidai naca dan zariya kufa?

A wani kauye kimanin shekaru dubu akayi wani' yaro #DanBaiwa, wato duk sanda akaje makabarta jana'ixa sai yaron yaga wata jar hula tataso daga kan mamacin tahau kan wani, duk kuma wanda tahau kansa tofa shine mai mutuwa nagaba agarin, da yaro yaga haka sai yasanar da liman. Baiyardaba, dafarko liman baiyardaba amma yaron yadinga fada masa. Wanda hular tahau kansu har mutum3 kuma duk suna mutuwa sai liman yasamu yaron yace masa don Allah duk sanda kaga hular tataho wajena kamin magana'' watarana anje makabarta anhaka Rami sai kasa tahau kan liman, yaron kuma yaga kasar don haka sai yakeso yasanar da liman don ya goge kasar kansa. Sai yaro yace liman...! Kanka.......! Ai bai ko karasaba da liman ya xabura aguje har yanzu ba'a samu labarinsa ba JAMA'A KO KUNGA LIMAN.?

GA WASU HANYOYI GUDA SHIDA WADANDA ZAKA IYA BINSU DON GYARA HALAYENKA :
1. Cikakken imani na gaskiya tare da yawaita neman kusanci da Allah

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.