Musha dariya :: ABIN MAMAKI BAYA KAREWA! - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Musha dariya :: ABIN MAMAKI BAYA KAREWA!

<
Wani saurayine yaje zance wajen budurwarsa , suna tsakiyar hira sai aka fara ruwa kamar da bakin kwarya har zuwa dare ruwa bai daukeba. sai baban yarinyar nan yace da ita "naga alama ruwannan ba mai daukewa bane yanzu,don haka ki gara masa dakin bakin nan sai ya kwana anan idan  Allah ya kaimu gobe sai ya koma. budurwar ta mike ta shiga gida don cika umarnin mahaifinta. bayan ta gama gyara dakin sai ta dawo don yiwa saurayin nata iso  amma abin mamaki sai ta tarar bayanan don haka ta koma ta sanar da babanta halin da ake ciki. uban ya rinka mamakin inda ya shiga ana cikin haka sai gashi ya shigo da gudu jikinsa ya jike jagab, da ganinshi sai uban ya tmbaye shi ina yaje haka cikin ruwannan? sai saurayin nan ya amsa da cewa"ai gida na koma na dwakko bargo saboda ko za'ayi sanyi cikin dare wai idan kaine uban yarinyar ya zakayi?

Wani yaro ne Budurwarsa ta gaiya ce shi Birth da y din ta sai yake tambayar Baban sa "me yakamata ya bata ?  Sai Baban yace "yaya Budurwar ta ke ? sai yaron ya fara fada masa  kamar haka :-
(1) Tana da kyau
(2) Tana da gashi
(3) Tana da Ido
(4) Ga ta siririya
(5) Ga jiki mai kyau
(6) Ga ta da Hips,
Kai Dad baka gan ta ba son kowa kin wanda ya rasa. Daga nan Baban yace kasan abin da za ka bata sai yaron yace a a. Sai Baban yace ka bata number ta .

Wani ustazu ne kullum yaje gurin budurwansa baida wani magana sai wa'azi ma'ana taji tsoron
allah ta bi duniya a hankali sai wannan budurwan tace ita ko sai ta gwada shi ta gani in mai tsoron
allah ne... dare nayi yazo gurin ta... suna cikin magana sai ta kama mai hannu..... ustazu yace "subhanallahi" ta rungume shi yace "alhamdulillahi" tai mai kiss yace masha'allah data sake shi yace astagfirullah.
Hahahhaha......!!! 

Wata amarya da mijinta sukaje bankin zenith domin su cire wani kudi. Ko da amarya tazo shiga se kawai muka ji wani alam me karfin gaske, jin haka se ga ‘yan sandan bankin su fito da gudu da bindigun su! Ai ina ganin haka se na tsure! Sun kamani ni da matata wai basu yarda damu ba shisa zasu kai ofishin ‘yan sanda sun bincike mu! Munje har anyi sacin dina amma basu ga komai ba! An zo kan matan ana sacin dinta kawai se ga gwangwanin milo babban ya fado daga kanta! Dani da ‘yan sandan ba wanda ze kama wani gurin gudu, domin kuwa mun dauka bom ne ya fado ashe wai acuci mazanta ne ya fado! Wannan jaraba dame yayi kama??? Shiko D.P.O be ma dawo cikin hayacin sa ba tsabar tsorata da yayi.

Jiya ina kwance da misalin karfe 2:30/am   na dare ina bacci sai na farka. Ina farkawa sai naji hayaniyar mutane a waje sai na fito amma banga kowa bahSai na koma daki na kwanta amma ban daina jin hayaniyar ba sai mah karuwa takeyi Na sake fitowa a karo na biyu but banga kowa bah.....Kamar ance in kalli sama,ina duba sama kuwa sai naga mutane Wai ashe jirgin sama ne ya lalace shine suke turawa Saura kuma kuce karya Nake.

Wata tsohuwa ce suka je kasuwa da karamin jikanta, sai jikan ya dauki motar wasa sai tsohuwa tace digiri ajiye motar nan, sai mai kaya ya tambayi tsohuwa: sunanshi digiri? Tsohuwa tace: mamanshi na tura   jami'a ta dawo min dashi

Wani bawan Allah ne mai tsananin kamun kai, wanda yake zaune a wani gidan haya da matarsa, sai watarana matarsa ta tafi unguwa shi kuma sai ya shiga bayi yayi wanka sai ya rataye tufafinsa akan katangar bayin don bayin budadde ne babu rufi. Sai wani 6arawo yaga tufafin sun leqo waje sai ya janyesu ya tsere ta lungu.
Mutumin bai tashi sanin an sace tufafinsa ba har sai da ya gama wankansa zai fito sannan ya ankara don haka sai ya tsaya shiru ya rasa abin yi don yaji motsin matar abokin zamansa tana kwashe shanyar tufafinta dafa shanya a igiyar shanyar dake tsakar gida kusa da bayin saboda tasowar iska kar ya zubar mata da tufafin. Ana cikin haka sai kuwa iskar ta dauki wani fallen zaninta ta jefa matashi bayi inda mutumin nan yake ciki.
Ai sai mutumin yayi murna ya dauki zanin matar wani ya daura don ya rufe tsiraicinsa dashi sai ya fito da sauri daure da zanin matar wani a qugunsa kuma gashi baya yin magana da matar auren gidan, sai ya nufi dakinsa da sauri ita kuwa mai zanin sai abun ya daure mata kai tana ta kallon zanin sallan da mijinta ya dinka mata a qugun wani mutum wanda ba mijinta ba.
Mutumin na isa dakinsa sai ya tuna ya ashe ya rufe dakin da makulli kuma makullin na cikin aljihun wandonsa da aka sace sai ya tsaya a jikin qofar yana salati don duk kayansa suna cikin dakin. Chan sai matarsa ta dawo unguwa taga mijinta da zanin matar hayar gidan sai ta tayar da rigima akan alanbalan yana neman matan gidan don su biyu aka bari a gidan kuma ga zani shaida a qugunsa don haka tabbas kwartanci yaje sukayi a dakinta har ya daura zaninta.
Ana cikin hayaniya sai mijin waccan matar da aka daura zaninta ya shigo yaga abin dake faruwa shima sai ya tayar da rigima har kotu da qyar Allah Ya fid da mutumin nan bisa shaidar tufafinsa da aka kaiwa wani dillali sayarwa shi kuma ya gane mai su don yasan ana rigimar shine ya kawosu kotu tare da yin cikakken bayanin da tasa aka kama 6arawon sannan aka wanke mutumin daga zargi.
*Ya Allah Ka qara tsaremu daga afkawa cikin kowane irin musibah, ameen.

***AN FASA KWAI***
Wani mutum ne yayi sabuwar amarya sai ya dauketa ya kaita wani hotel don suyi honey moon dinsu a chan, watau suci amarcinsu a tsanake inji sa'ad khalifa yakubu (sky) .
suna shiga hotel din sai mutumin ya ajiye amaryar tasa a falo don yaje reception ya biya kudin daki ya kar6o makulli. Zaman amaryar keda wuya sai wata karuwa tazo wurinta ta sameta tace "sannu 'yar-uwa naga waccan macucin mutumin kema ya kawoki nan ne ku kwana (ta nuna mijin) toh kar ki sake ya kwana dake bai biyaki ba (ta dauka itama karuwa ce) kiyi maza ki amshi kudinki tun da farko don guduwa yakeyi baya biya don ni shaida ce saboda munsha kwana dashi baya biyana. kuma ki tambayi kowace karuwa a hotel dinnan kiji don kusan duk ya nemesu suna kwana dashi yana guduwa baya biya. kema don naga baquwa ce baki san halinshi bane har kika biyoshi zaku kwana ya cuceki. gashi da shegen neman karuwan tsiya kamar bunsuru don ni tuni ai na gujeshi kar yasa mun qanjamau don naji ana rade-radin wai yanzu ya kamu da qanjaman don cikakken 'Dan-duniya ne"
*Wai in kece amaryar ya za kiyi tun baku tare ba? za kiyi kasada ne ku kwana sannan ki tabbatar ko kuwa ya ya???
*KIWON LAFIYA
(yadda zaka cire targade da kanka)
Ka sami igiyar kyalle mai karfi sai ka daure yatsar mai targade a wani turke kamar na rumfa, sai ka fizgi yatsan da karfi fizga daya idan kayi da kyau targaden zai fita. Yadda zaka gane fitarsa shine za kaji yayi qara 'qas' alamar ya fita ya gyaru kenan, sai ka sami mantaleta ka dirza a wurin targaden. Da safe ka gasa da ruwan zafi da tawul kasa mantaleta shikenan. Idan bai fita ba yayi qara ba sai ka sake kwatantawa har a dace shikenan.

BAZAZZAGI DA LARABCI.
Wani Bazazzagi ne suka hada kudi da Balarabe suka sayi jakai guda
biyu suna kiwo. Kuma ya kasance Bazazzagi ke yin kiwon wadannan
jakuna guda 2. Kwatsam wata rana sai aka yi ruwa ya cika gidan Bazazzagin nan, har jakunan suka mutu. Ya je ya samu Balarabe, yana so ya yi masa Bayanin cewa ruwa ya cika masa gida har jakunan sun mutu. Suna haduwa sai ya ce masa: “Wa himaruka wa himariy, al ma’u bulbula fiy baitiy, mautu jami’an.”

SAI IN ZAMA 'DAN TASI KAMAR KA!
Wani dan tasi ne ya dauko yara daga makaranta, sai wani daga cikinsu ya yi ta surutu, yana karatun da aka koya masu a ranar, yana cewa: “Idan babana sarki ne, mamata sarauniya, zan zama yarima.” dan tasi ya damu kwarai,
sai ya ce wa yaron: “Idan babanka dan fashi ne fa, kuma innarka karuwa, kai kuma me za ka zama?” Sai (yaro) ya ce: “Sai in zama dan tasi kamarka!”

wani saurayi ne yana zaune a gaban gidan su sai yaga wata yarinya taxo xata wuce yana ganin ta sai yaji ta kwanta mishi aransa ae kuwa baiyi kasa a gwiwa ba yaje yayi mata sallama ta amsa mishi sai yace baiwar Allah idan baxa ki damu ba ina dan so ki bani 1minute xan danyi magana dake ne sai tace ba damuwa.... Malama agaskia baxan 6oye miki ba tunda na ganki sai naji kinyi min ma'ana naji ina matukar son ki a raina.... Idan baxa ki damu ba xanso naji sunan malaman... Kuma xanso da ki bani full Address naki... Tayi shiru na dan wasu seconds ba tare da tace komai ba... Tana juyo wa sai ta daga hannu ta shimfida masa mari tace haba malam ka kalle ni ka kalle ka kace wai ni kake so plz na wuce da sanin ka kaje ka nemi dai-dai dakai.... Ba tare da yace mata komai ba sai ya juya ya tafi abin yayi masa matukar ciwo a xuciyar sa amman haka ya danne xuciyarsa.... bayan kamar 2weeks haka yana xaune a gaban gida inda ya saba xama sai yaji anyi masa sallama cikin wata sassanyar murya sai ya amsa sallaman sannan kuma ya daga kansa domin ganin wanda yayi masa sallaman yana daga kansa sai yaga Ashe wannan yarinya ce wanda ya ta6a tare wa 2weeks da suka wuce... Sai tace bawan Allah nasan xa kayi mamakin gani na amman kuma ba abin mamaki bane... Tun randa wannan abu ya faru na kasa samun sukuni a cikin xuciyata... Na kuma kasa samun nutsuwa araina... Sai naji cikin ikon Allah bayan faruwar wannan Abu sainaji na kamu da son ka araina... kuma ni yanxu nayi nadama abin da nayi maka plz ina so ka yafe min kuma ina so ka amsa soyayyah ta.... Wai yanxu idan kaine hakan ta faru da kai wani irin Answer za ka bawa wannan yarinyar...???


A BIYO MU A LITTAFI NA GABA.
Wani mai share cikin jirgin sama ne mai karambani bayan ya shiga jirgi don yin goge-goge kamar yadda ya saba, sai ya tarar da wani littafi mai taken: “YADDA AKE KOYON TUkIN JIRGIN SAMA A SAUkAkE.”
Yana bude shafin farko sai ya ga an rubutu “Idan aka danna, kaza da kaza, za a tayar da injin jirgi. Sai ya danna, injin jirgi ya fara aiki. Sai ya bude shafi na gaba, nan kuma aka rubuta “Idan aka danna kaza da kaza, jirgi zai fara tafiya, nan ma ya danna, jirgi ya fara tafiya.
Can da ya bude shafi na gaba, sai ya ga an rubutu “Idan aka danna kaza da kaza jirgi zai yi sama, nan ma ya danna jirgi ya tashi sama da shi. Da ya bude shafi na gaba, sai idonsa ya raina fata don ya ga an rubuta “Don jin yadda jirgi ke sauka sai a biyo mu a littafi na gaba!”

SAURAYI DA BUDURWA 1.
Wani saurayi ne da budurwarsa suka yi hira kamar haka:
Saurayi: Ladidi an tashi lafiya?
Budurwa: Ta yi biris kamar ba ta ji shi ba.
Saurayi: Ladidi an kusa daura mana aure amma har yanzu ba ki daina yi min wulakanci ba.
Budurwa: Ta sake biris.
Saurayi: Dama ba wani abu ne ya kawo ni ba illa in tambaye ki ko kin iya tuki. Domin ina son matata ta kware a tuki
Budurwa: Nan da nan ta amsa cewa Tanimu ke nan shi ya sa nake matukar sonka.
Saurayi: Uhmm…
Budurwa: To wace irin mota za ka saya min?
Saurayi: Mota kuma?
Budurwa: Eh mana, ba yanzu ka tambaye ni ko na iya tuki ba?
Saurayi: Ni fa tukin tuwo nake nufi don wani masoyina ne ya ba ni kyautar buhun masara.


ZANI KO ISHMAWY?
Wani Bagobiri ne matarsa ta shiga Islamiyya, rannan ta dawo daga makarantar, ta zauna kenan sai ga mijin nata ya dawo daga aiki. Kafin ma ya huta sai ta ce masa: "Maigida, ina so ka sayo mini Ishmawy." Shi kuwa sai ya kama muzurai irin na mazan nan masu nuna iko, ya ce mata: "Yadi nawa zai ishe ki d'inkawa?" Shi a zatonsa, Ishmawy zani ne, bai san littafin ba ne na addini.

'YAR SOJA.
Wani mahaukaci ne da ya saba cin kayan yara ba tare da ya biya ba, yakan tare yaran da aka doro wa talla ya amsa da karfi ya cinye. Rannan sai ya ci kayan wata diyar soja, ta koma gida tana kuka, babanta ya turo sojoji suka kama shi suka fara casa shi. Nan da nan ya fara kururuwa, yana cewa: “Jama’a ku taimaka, kuna ganin mahaukata suna duka na, idan kuka kyale su za su kashe ni, domin ba su da hankali.”


KISHIN MATA!
Wani mutum ne tare da matarsa, rayuwa ta yi masa zafi, ya fara hayar da babur. Wata rana ya ci karo da wani tsohon abokinsa attaijri, yana cikin hamshakiyar mota. Attajirin ya ga halin da yake ciki, ya ba shi cekin Banki na Naira miliyan 10. Saboda murna, ko adireshe ko lambar waya bai amsa ba, haka suka rabu ya tafi gida yana murna. Yana zuwa gida suka zauna da matarsa, domin tsara yadda za su kashe kudin. Ga yadda ta kaya:
“Za mu sayi gida. Za mu sanya ’ya’yanmu makarantar kudi. Za mu sayi mota. Zan saya miki kayan alatu. Zan kara aure.” Yana fadin haka, sai ta shammace shi ta fisge cekin kudin daga hannunsa ta jefa a bakinta ta taune, ta hadiye. Ga shi bai san inda zai kara ganin abokin nan nasa ba!
IDAN KAI NE MIJIN YA ZA KA YI?

ZA A YI SANYI!
Wani Bazazzage ne ya je wurin budurwarsa, suna cikin hira sai kawai hadari ya taso. Kafin ka ce me, an fara ruwan sama mai karfin gaske. Ganin haka sai baban yarinyar ya fito daga gida, ya ce mata: “Da alamu wannan ruwan ba mai tsagaitawa ba ne, watakila a kwana ana yi. Ki shiga ki gyara masa dakin baki, da safe sai ya tafi.” Nan da nan ta shiga gida ta fara gyara daki, tana gamawa sai suka fito ba su ga Bazazzage ba. Can sai ga shi nan ya shigo a guje, ya jike jagaf. Sai baban ya tambaye shi cewa: “Daga ina haka?” Sai saurayin ya ce: “Gidanmu na je na dauko bargona saboda na san za a yi sanyi cikin dare.”


GODIYAR ANGO.
Wani ango ne ana walimar bikinsa a gaban ’yan uwa da abokan arziki, bayan an kammala sai aka ce ya tashi ya yi jawabin godiya. ANGO: Godiya ga Malam Hashimu dillalin gidaje, wanda ya ba mu aron gidan da za mu zauna kafin mu samu na haya. Ba zana taba mantawa da Hajiya Tasallah Mai Adashi ba, wadda ta ba ni daukar farko don in kai kudin auren. Godiya ga Asabe Dillaliya, wadda ta ba mu bashin atamfofi da shaddodi da muka saka a lefe. Allah Ya saka wa kanwata Basariyya, da taimakonta ne na fita kunya, inda ta ba mu aron akwatunan lefenta muka saka kayan a ciki, bisa yarjejeniyar mayarwa bayan an gama biki da mako 2. Allah Ya bar zumunci, Ya ba mu ikon cika alkwurran da muka dauka. Ba zan manta Atiku Mai Wanki Da Guga ba, da ya ba ni aron kaya domin in saka a wannan rana. Mun gode.


WATA MAGE.
Wani mutum ne matarsa ke da mage, kullum ta dame su da barna. Wata rana sai ya dauke ta,
ya yi tafiya mai nisa da ita cikin daji da motarsa. Ya aje motar, ya dauki magen ya yi tafiya mai nisa da ita cikin dajin nan, ya jefar da ita. Ya kama hanyar dawowa sai ya yi makuwa, ya rasa inda ya aje motar.
Tun safe yake tafiya har La’asar bai kai ga inda ya aje motar ba, sai ya buga wa matarsa waya, ya sanar da ita halin da yake ciki. Matarsa ta ce: “Ai kuwa bayan tafiyarka da awa biyu sai ga magen ta dawo gida.” Shi kuwa sai ya kara rudewa, ya ce wa matar: “Ba magen waya mu yi magana da ita”

'DANGOTE NAKE SO.
Wani Inyamuri ne ya je wajen mai
tafsiri ya ce zai musulunta. Bayan
an gama dora masa kalmar shahada, aka tambaye shi ko wane suna yake so. Ya tambayi a zana masa misalan sunayen Musulunci, aka ce masa akwai Ibrahim ko Nuhu ko Isa ko Yahaya ko Aminu da sauransu. Kun san Inyamuri da son kudi, ko da ya ji haka sai ya yi murmushi, ya ce: “Cikin sunayen ban ji an hada da dangote ba. Ni sunan nake so a rada mani.”

GORIBAR KANO!
Wani Bazazzagi ne dan uwansa yana zaune a Kano, sai ya kai masa ziyara. Yana zuwa ya tare shi da farin ciki da fara’a, ya ba shi ruwa mai sanyi ya sha. Bayan ya huta
sai ya kawo masa kayan marmari, ciki har da tuffa ja.
Da ya É—auki tuffa ya gatsa, sai ya ce: “Kano komai nasu daban ne, tun da nake a duniya ban taba cin goriba mai laushi da zaki kamar
wannan ba. Ashe cutarmu ake a Zariya!”

MATSORACIYAR DALIBA!
Wata rana malamin makarantar boko ya bai wa dalibai jarabawar da za su yi a gida, ya ce kowa ya zana hoton wani abu sai a kawo gobe. Bayan sun kawo washegari sai malamin yana dubawa can ya lura da cewa wata daliba ba ta zana komai ba a takardarta, sunanta ne kawai ta rubuta. Sai malamin ya tambaye ta dalilin da ba ta zana komai ba. Ita kuma tana tsoron malamin sosai, sai ta ce: "Wallahi malam na zana hoton jaki yana cin ciyawa, watakila ya cinye ya yi tafiyarsa."
Idan kai ne malamin me za ka yi mata?

CAJIN WAYA!
Wata rana wani Bakano ya je bakunta Zariya, yana shiga garin, kawai sai ya ga mutane sai gudu suke yi. To abinka da bako, bai san me yake faruwa ba, kawai shi ma sai ya shiga sahun masu gudu.
Ana cikin gudu to sai ya ga kowa da ya zo kofar gidansa sai ya ga kawai ya shiga, kuma ba tare da ya rufe kofa ba. Ya duba ya ga yadda kowa ya fita daga hayyacinsa, ana ta gudu.
Kawai sai ya yanke shawarar, ya rike daya ya tambaye shi. Yana juyawa sai ya rike na gefensa, ya ce masa: “Wai gudun me ake yi ne? Sai mutumin nan ya ce: “Ai wutar NEPA aka kawo, shi ne kowa yake gudu ya je ya saka cajin waya.”

SATAR AKUYAR TSOHUWA.
Wani 6arawo ne yaje sata gidan wata tsohuwa. Bayan ya yi sa'a ya saci akuyar ya kai kasuwa ya sayar naira dubu shida, sai ya laluba jakar sa domin ya hada kudin da na aljihunsa, ashe ya yi rashin sa'a ya zubar da naira dubu ashirin a gidan tsohuwa.
Fitowar tsohuwa ke da wuya sai ta ga ba akuya amma ga daurin kudi a aje kusa da tirken akuya. Tsohuwa ta dauka ta godewa Allah.
Ba jimawa kawai sai ga 6arawon ya dawo gidan sai ya tarar da tsohuwa zaune tana kirga kudi, sai 6arawo ya yi qarfin halin gaisheta, ta kuma amsa mishi. Sai 6arawo ya ce "wallahi Inna akuyar ma dubu shida aka siyar da ita". Sai tsohuwa ta ce "eh haka sha'anin kasuwa yake, yau riba gobe faduwa.


ABIN MAMAKI BAYA KAREWA!
China ta hada wani machine mai kama barayi, da aka kai shi America cikin minti 20 ya kama mutun 30, da aka kai shi England cikin minti 40 ya kama mutum 250, da aka kai shi Saudiya cikin kwana 8 ya kama mutun 2, da aka kai shi Ghana cikin kwana 1 ya kama mutum 2000, da aka kai shi Cameroon cikin minti 20 ya kama mutum 1500, da aka kai shi Nigeria cikin minti 3 aka sace machine din.


SABODA KUDI!
Wata yarinya ce aka yi wa cikin shege, mahaifinta da mahaifiyarta suka kama dukanta suna cewa ta gaya musu wanda ya yi mata shi. Yarinyar ta ce wani mai kudi ne na shiyyarsu yayi mata shi. Da aka je aka kira mai kudin, aka tambaye shi, sai ya kyale su har sau uku, sannan ya ce: “Ni ne na yi mata. Idan ta haifi namiji zan ba babanta Naira miliyan 5, mahaifiyarta Naira miliyan 3, yarinyar kuma Naira miliyan 2. Idan kuma ta haifi mace, zan ba babanta Naira miliyan 3, innarta Naira miliyan 2, ita kuma yarinyar Naira miliyan 3” Ya ci gaba da cewa: “Idan kuma cikin ya zube…” Bai ida maganarsa ba sai baban yarinyar ya yi farat ya ce: “Sai ka sake yi mata wani cikin!”

GUDUN NI'IMA.
Wani mutun ne ya ga hadari ya hadu, gari ya yi baki kirin sai ya kama hanyar gida yana ta sauri. Sai suka hadu da wani mutum, ya ce: “Malam, ni’imar Allah za ta sauka kake gudunta?” Sai mutumin nan ya daina sauri, ruwan ya sauka ya yi masa dukan tsiya. Rannan yana zaune sai ya ga wannan mutumin da ya hana shi sauri yana ta sauri saboda ya ga hadari. Ya ce: “Malam rahama za ta sauka kana gudunta?” Sai ya ce: “Ina gudu don kada in taka rahamar ne.”

MASU HAIHUWA.
Wasu mutane ne su uku, suka kai matansa asibiti domin haihuwa, daya ma’aikacin kamfanin 2 Effects ne, daya ma’aikacin kamfanin 3 Crowns, daya kuma ma’aikacin kamfani 7Up ne. Suna zaune suna hira, suna jiran sakamakon matansu sai ga nas ta fito, ta ce: “Ina ma’aikacin 2 Effects?” Da ya ce ga shi sai ta ce masa: “An samu ’yan biyu.” Ya kama murna. Bayan ta shiga ta sake dawowa, ta ce: “Ina ma’aikacin 3 Crowns?” Ta ce masa: “An samu ’yan uku.” Da ta koma ciki, bayan kimanin miti biyar sai ta dawo, ta ce: “Ina ma’aikacin 7Up?” Sai ya kama kuka, yana tsammanin ’ya’ya bakwai matarsa ta haifa, ya ce: “Wayyo Allah, ga ni!” Sai ta ce masa: “An samu da daya amma ya koma.” Nan take sai ya ce: “Alhamdu lillahi!”

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.