Labaran wasanni::::::: Modric ya lashe kyautar gwarzon Balkan - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran wasanni::::::: Modric ya lashe kyautar gwarzon Balkan

<
Dan wasan Real Madrid, Luka Modric ya lashe kyautar
gwarzon dan wasan kudu maso yammacin Turai na shekarar
2018, wato Balkan Athlete of the year.

Modric dan kasar Croatia shi ne dan kwallon kafa na biyu da
ya ci kyautar, bayan Hristo Stoichkov gwarzon dan kwallon
kafar nahiyar Turai a shekarar 1994.

Dan wasan mai shekara 33 ya yi nasara ne da maki 77 a biki
na 46 da kamfanin yada labarai na Bulgaria (BTA) kan
gudanar, ya kuma doke Novak Djokovic wanda ya jera karo
biyar yana lashe kyautar tun daga 2011 zuwa 2015.

Modric shi ne ya lashe kyautar Ballon d'Or ya kuma ci kofin
Zakarun Turai da na Zakarun nahiyoyin duniya da Real Madrid,
ya kuma kai Croatia wasan karshe a kofin duniya shi ne
gwarzon gasar a Rasha.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.