Labaran wasanni::::: 'Liverpool za ta lashe Premier ba a doke ta ba' - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran wasanni::::: 'Liverpool za ta lashe Premier ba a doke ta ba'

<
Kocin Arsenal, Unai Emery ya ce Liverpool za ta bi sawun
Gunners na lashe kofin Premier ba tare da an doke ta ba a
kakar shekarar nan.


Arsenal za ta ziyarci Anfield a ranar Asabar a gasar Premier
wasan mako na 20, Liverpool tana ta daya a kan teburin da
tazarar maki shida, kuma har yanzu babu kungiyar da ta doke
ta a bana.


Liverpool ta yi nasarar cin wasa takwas a jere tun 2-2 da ta yi
da Arsenal a Emirates a ranar 3 ga watan Nuwamba.
Arsenal ce a cikin karnin nan ta lashe kofin Premier ba tare da
an doke ta ba a kakar 2004, karkashin Arsene Wenger.
Emery ya ce yana ganin Liverpool za ta iya lashe Premier
shekarar nan ba tare da an doke ta ba, domin tana da 'yan
wasan da za su kai kungiyar ga yin nasara.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.