Labaran siyasar chikin kasa Nigeria :: wai Maine gaskia labarineBa gaskiya bane cewar Dangote na cikin kungiyar yakin zaben Buhari - Fadar shugaban kasa shine da gaske ko yaya ? - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran siyasar chikin kasa Nigeria :: wai Maine gaskia labarineBa gaskiya bane cewar Dangote na cikin kungiyar yakin zaben Buhari - Fadar shugaban kasa shine da gaske ko yaya ?

<
Fadar shugaban kasa, ta fito ta karyata wani rahoto da Femi Adesina ya fitar, na cewar Aliko Dangote na daga cikin mambobin kwamitin yakin zaben Buhari
- Fadar shugaban kasar ta ce akwai muhimmancin fayyacewa 'yan Nigeria gaskiya kan matsayar Dangote a cikin harkokin kwamitin yakin zaben shugaban kasar
- Haka zaika, fadar shugaban kasar ta ce Dangote bai da katin shaidar zama dan jam'iyyar APC, don haka ba zai taba zama mamba na wannan kwamiti na PCC ba
Bayan sanya sunan hamshakin dan kasuwa, kuwa wanda yafi kowa kudi a Afrika, Aliko Dangote, a cikin mambobin kwamitin mashawarta na yakin zaben shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC, fadar shugaban kasa yanzu ta ce Dangote baya daga cikin mambobin wannan kwamiti.
A cikin wata sanarwa kan batun kafa kwamitin wada Femi Adesina ya rabawa manema labarai a ranar Juma'a, ya sanya sunan Atiku a cikin jerin sunayen mambobin kwamitin wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ke a matsayin shugaba, yayin da Asiwaju Bola Tinubum Sanata Ahmed Lawan (shugaban masu rinjaye a majalisar dattijai), Hon Femi Gbajabiamila (shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan tarayya) da kuma shugaban APC na kasa, Adams Oshiomole a matsayin mambobi.
Ba gaskiya bane cewar Dangote na cikin kungiyar yakin zaben Buhari - Fadar shugaban kasa
Ba gaskiya bane cewar Dangote na cikin kungiyar yakin zaben Buhari - Fadar shugaban kasa
Sai dai a cikin wata sanarwa daga kakakin fadar shugaban kasa, da ya rabawa manema labarai a daren ranar Juma'a, na cewa: "Hakika zai zama abu mai matukar muhimmanci, wayar da kan jama'a dangane da sanya sunan Alhaji Aliko Dangote, a cikin mambobin kwmaitin mashawarta na kungiyar yakin zaben shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC, kamar yadda wata sanarwa ta gabata a ranar Juma'a 28 ga watan Disambar 2018.
"Wanda yafi kowa kudi a Afrika, baya daga cikin mamallaka katin shaidar zama dan jam'iyyar APC, don haka ba zai taba zama mamba na wannan kwamiti na PCC ba. Haka zalika bashi daga cikin mambobin kwamitin zaman lafiya na jam'iyyar, don haka, ba zai iya tsoma hannunsa a cikin harkokij yakin zaben kwamitin da jam'iyyar ba."

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.