Labaran siyasa Nigeria ::: Kin sanya hannu a dokar zabe: Yan takarar shugaban kasa sun marawa Buhari baya - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran siyasa Nigeria ::: Kin sanya hannu a dokar zabe: Yan takarar shugaban kasa sun marawa Buhari baya

<
Kungiyar yan takarar kujeran shugabancin kasa sun marawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari baya akan kin sanya hannu a gyararren dokar zabe na 2018-
 Sun yanke wannan shawarar ne a wani ganawa da suka yi domin sake duba lamarin.
- Yan takarar shugabancin kasar 40 a karkashin kungiyar sun bayyana cewa sun marawa matsayar Buhari baya na kin sanya hannu a dokar domin yayi kusa da yawa da zabe kasa mai zuwa
Kungiyar yan takarar kujeran shugabancin kasa a ranar Lahadi, 9 ga watan Disamba sun marawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari baya akan kin sanya hannu a gyararren dokar zabe na 2018.
Kungiyar ta yanke wannan shawarar ne a wani ganawa da suka yi domin sake duba lamarin.
A cewar wata sanarwa daga majiyarmu, yan takarar shugabancin kasar 40 a karkashin kungiyar sun bayyana cewa sun marawa matsayar Buhari baya na kin sanya hannu a dokar domin yayi kusa da yawa da zabe kasa mai zuwa.
Kin sanya hannu a dokar zabe: Yan takarar shugaban kasa sun marawa Buhari baya
Kin sanya hannu a dokar zabe: Yan takarar shugaban kasa sun marawa Buhari baya
Sanarwar na dauke da sanya hannun yan takarar jam’iyyun Peoples Democratic Alliance, Alhaji Shitu Kabir; da na Movement for the Restoration of Democracy, Danjuma Muhammad.
Ga yadda sanarwar ya zo: “Lokacin da ya rage daga yanzu zuwa zaben 2019 ya yi gajartan da INEC zata kwashi ma’aikata sannan ta basu horon da ya kamata.
“Sannan muna tunanin cewa hukumar zaben na iya kin yin sauri a wararen da na’ura suka ki aiki.
“Da gangan hakan na iya hana wasu al’umman karkara samun damar yin zabe.”

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.