Labaran siyasa chikin kasa Nigeria. :: Wajibi ne Najeriya ta taimakawa ECOWAS - Buhari - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran siyasa chikin kasa Nigeria. :: Wajibi ne Najeriya ta taimakawa ECOWAS - Buhari

<
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba kungiyar kasashen Afrika ta yamma (ECOWAS) tabbacin cewa kasar Najeriya za ta ci gaba da tallafawa yankunan da ke kungiyar. Ya bayar da tabbacin ne lokacin da ya karbi bakuncin wata tawaga karkashin jagorancin kakakin majalisar ECOWAS, Moustapha Cisse Lo.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba kungiyar kasashen Afrika ta yamma (ECOWAS) tabbacin cewa kasar Najeriya za ta ci gaba da tallafawa yankunan da ke kungiyar.
Ya bayar da tabbacin ne lokacin da ya karbi bakuncin wata tawaga karkashin jagorancin kakakin majalisar ECOWAS, Moustapha Cisse Lo, a ranar Alhamis, 13 ga watan Disama a fadar shugaba kasa da ke Abuja.
Wajibi ne Najeriya ta taimakawa ECOWAS - Buhari
Wajibi ne Najeriya ta taimakawa ECOWAS - Buhari
“Kasancewa na shugaban kasar Najeriya kuma shugaban kasashen ECOWAS, wajibi ne ga Najeriya ta taimakawa kungiyar,” kamar yadda shugaban kasar ya bayyana a wata sanarwa daga mai bashi shawara a harkar labarai, Femi Adesina.
Furucin shugaan kasar martani ne ga bukatar kakakin kungiyar, wanda suka hada da masauki, biyan alawus, da kuma sauran lamaran day a shafi jin dadinsu.
Ya kara da cewa, “Zamu kula da lamarin. Hakkinmu ne kula da ku. Zamu duba lamuran da suka gabatar.”
Kakakin majalisar Cisse Lo ya gode ma kasar Najeriya da ta bayar da fili a Abuja ga majalisar ECOWAS domin gina sakatariyarta na din-din-din.
Ya kuma yabama gwamnati mai ci kan jajircewarta a harkar tsaro da yaki da cin hanci da rashawa.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.