Labaran shiyasa:: 'Yan takarar mataimakin shugaban Najeriya Osinbajo da Peter Obi za su yi muhawara - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran shiyasa:: 'Yan takarar mataimakin shugaban Najeriya Osinbajo da Peter Obi za su yi muhawara

<  
Ranar Juma'a ake sa ran 'yan takarar mataimakin shugaban
kasar Najeriya za su tafka muhawara kan zaben 2019.
Muhawarar, wacce wata kungiya mai suna the Nigerian
Election Debate Group, NEDG, da kuma the Broadcasting
Organisations of Nigeria, BON suka shirya a Abuja, za ta mayar
da hankali ne kan irin shirye-shiryen da 'yan takarar ke da su
wurin inganta rayuwar 'yan Najeriya.
Ana sa ran 'yan takarar mataimakin shugaban kasa biyar za su
halarci muhawarar.
'Yan takarar su ne: Yemi Osinbajo (APC), Peter Obi (PDP),
Umma Getso (YPP), Alhaji Abdulganiyu Galadima (ACPN) da
kuma Khadijah Abdullahi-Iya (ANN).
Shugaban BON, John Momoh, ya ce za a watsa muhawarar
kai-tsaye a dukkan tasoshin BON (NTA, Channels TV, AIT,
Silverbird TV, da sauran su ya kara da cewa za a iya kallon muhawarar kai-tsaye a
Facebook da YouTube da kuma Twitter.
Jam'iyyar APC mai mulkin kasar ta ce ta taka rawar gani wajen
inganta rayuwar 'yan Najeriya shi ya sa take neman ci gaba da
mulki a 2019.
Sai dai jam'iyyun hamayya, musamman PDP, sun sha cewa
gwamnatin Shugaba Buhari ta gaza kawo sauyin da ta yi wa
'yan kasar alkawari gabanin zaben 2015.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.