Labaran Najeriya::: Takaitaccen tarihin Alhaji Shehu Shagari - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran Najeriya::: Takaitaccen tarihin Alhaji Shehu Shagari

<
Mun sake wallafa muku wannan makala ne a karo na biyu
sakamakon rasuwar Alhaji Shehu Shagari. Mun fara wallafa ta a
ranar 16 ga Satumbar 2010.
An haifi Alhaji Shehu Shagari a kauyen Shagari a shekarar
1925, kuma shi ne da na shida ga mahaifinsa Aliyu, magajin
kauyen Shagari, wanda manomi ne, dan kasuwa yana kuma
kiwo.
Allah ya yi wa mahifinsa rasuwa yana dan shekara biyar da
haihuwa.
Alhaji Shehu Shagari ya fara karatun kur'ani tun yana dan
shekara hudu, kuma daga bisani ya je makarantar Elimentari
da ke garin Yabo kusa da kauyen Shagari, daga nan kuma ya
tafi makarantar Middle a Sokoto, daga nan kuma ya je kwaleji
ta Kaduna.
Bayan da ya kammala karatun sakandirensa, Alhaji Shehu
Shagari ya yi koyarwa a makarantun middle daban-daban a
matsayin malamin kimiyya da ma tarihi.
Tun yana kwaleji, Shagari ya fara nuna sha'awar shiga siyasa,
inda a shekarar 1946 shi da Malam Gambo Abuja suka kafa
wata kungiyar matasa a Sokoto, kuma sun samu goyan bayan
dattijai kamar Sir Ahmadu Bello da Ibrahim Gusau da kuma
Malam Ahmadu Dabbaba.
A shekarar 1948 ne kuma aka amince da a hade dukkanin
kungiyoyin siyasar yankin zuwa kungiyar NPC wadda daga
bisani ta zama jam'iyyar da ta tsaya takara a zaben shekarar
1959.
Kafin wannan shekarar ne aka zabi Shagari a matsayin wakilin
mazabar Kudu-maso Kudancin Sokoto, kuma a shekarar 1958,
an zabe shi a matsayin sakataren majalisar Firaminista, Sir
Abubakar Tafawa Balewa.
Daga bisani Shagari ya rike mukaman minista daban-daban da
suka hada da na ci gaban tattalin arziki (1960), da na kula da
harkokin cikin gida (1962) da kuma na ayyuka da safiyo (1965).
Bayan juyin mulkin farko da sojoji suka yi, Alhaji Shehu Shagari
ya koma gida Sokoto.
Da hawan janar Gowon ya bai wa Shagari ministan kula da
harkokin tattalin arziki, daga bisani kuma aka ba shi ministan
kudi.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.