labaran duniya: Tsohon shugaban Amurka George Bush ya mutu - BESTAREWA BlOG

Header Ads

labaran duniya: Tsohon shugaban Amurka George Bush ya mutu

<
Tsohon shugaban Amurka George Bush ya mutu yana da
shekara 94 da haihuwa. Dansa George W Bush ne ya fitar da
wannan sanarwar.
Tsohon shugaban da aka fi sani da George Bush Senior ya
mutu ne ranar Juma'a da yamma kamar yadda wani kakakin
iyalin gidansa ya bayyana.
Shi ne shugaban Amurka na 41 tsakanin shekarar 1989 da 1993
bayan ya shafe shekara takwas a matsayin mataimakin
shugaban kasa Ronald Reagan.
Amma duk kasancewa farin jininsa ya kai kashi 90 cikin 100,
an tuhume shi da rashin kulawa da harkokin cikin gida, inda Bill
Clinton ya kayar da shi a zaben 1992.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.