Labaran Duniya :: mai yasa akakaii Facebook kara kan bayanan jama'a a Amurka - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran Duniya :: mai yasa akakaii Facebook kara kan bayanan jama'a a Amurka

<
Babban mai shigar da kara a birnin Washington ya yi karar Facebook a kotu, a karon farko a kokarin hukunta shafin a kan rawar da ya taka a rikicin Cambridge Analytica.
Karl Racine ya kai karar ne ranar Laraba kamar yadda jaridar Washington Post ta ruwaito.
Facebook ya shiga yarjejeniyar sirri kan bayanan mabiyansa
'An saci bayanan mutane miliyan 50 a Facebook'
Facebook ya sami matsala ta gajeren lokaci
Jaridar ta zargi Facebook da barin bayanan miliyoyin masu amfani da shafin a bayyane.
Wannan ya zo ne bayan bincike da yawa da ake gudanarwa bayan matsalolin tsaro a kan shafin.
Jami'i mai hulda da jama'a na Facebook ya bayyana wa BBC cewa "Muna duba korafin kuma muna shirin ci gaba da tattaunawa da babban Atoni Janar na birnin Washington DC da ma sauran wurare"
A Birtaniya, an ci tarar kamfanin pan 500,000 kan rikicin na Cambridge Analytica.
Wannan ita ce tara mafi yawa da mahukuntan za su iya daurawa a Birtaniyu

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.