Labaran duniya::: Khashoggi da wasu 'yan jaridu ne 'Gwarzayen Shekarar 2018' - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran duniya::: Khashoggi da wasu 'yan jaridu ne 'Gwarzayen Shekarar 2018'

<
Mujallar Time ta zabi 'yan jaridar da aka kashe ko ake tsare
da su a matsayin gwarzayen shekara ta 2018.
Mujallar ta wallafa shafukanta na farko guda hudu inda aka sa
'yan jaridun da hukumomi suka sa a gaba saboda aikin da suke
yi a bana.

Sun hada da Jamal Khashoggi wanda aka kashe a karamin
ofishin jakadancin Saudiyya da ke Turkiyya
Wasu 'yan jarida masu aiki a jaridar nan ta Amurka mai suna
Capital Gazette inda aka kashe wasu abokan aikinsu biyar
suma sun sami shiga jerin gwarzayen shekara tare da Maria
Ressa ta kasar Filifins da kuma matan 'yan jaridan Myanmar
Wa Lone da Kyaw Soe Oo.

Mujallar Time ta ce ta zabe su ne saboda "sadaukar da
rayukansu da suka yi domin fayyace gaskiya, da kuma kokarin
da suke yi na bayyana zahirin abubuwan da ke faruwa".
Su waye 'yan jaridar?

Jamal Khashoggi

Jamal Khashoggi sanannan dan jarida ne dan kasar Saudiyya
wanda kuma ke sukar hukumomin kasarsa. Ya bace bayan da
ya ziyarci ofishin jakadancin Saudiyyar da ke birnin Santanbul
na kasar Turkiyya a watan Oktoba.
Mista Khashoggi na gudun hijira a Amurka ne, inda yake aiki
da jaridar Washington Post. Ya tafi birnin Santanbul ne domin
karban takardu dangane da auren wata budurwarsa 'yar
Turkiyya da yake son yi.

Ma'aikatan jaridar Capital Gazette

A ranar 28 ga watan Yuli wani dan bindiga ya shiga ofishin
jaridar Capital Gazette a birnin Annapolis da ke jihar Maryland
inda ya kashe ma'aikatan jaridar su biyar.,
Daga baya bincike ya nuna cewa dan bindigar na hakon jaridar
na dadadden lokaci bayan da ya kasa sa wata kotu ta biya shi
diyya kan wata kara da ya kai jaridar a shekarar 2012.
Amma wannan tashin hankalin bai hana ma'aikatan ci gaba da
aiki daga filin da ake ajiye motoci ba, wanda ya sanya suka iya
wallafa jaridar da ta fita kashegari.
Ban da wallafa sakonnin mutuwar abokan aikinsu, sun bar
shafin da ake wallafa sharhi fayau babu rubutu saboda ba su
da abin cewa, kamar yadda suka wallafa.

Maria Ressa da Rappler

Tsohuwar 'yar jaridar tashar CNN Maria Ressa ta samar da
shafin labarai na intanet mai suna Rappler a kasar Filipins a
shekara 2012, kuma ba a dade ba ta yi fice saboda ingantattun
labaran da take samarwa.

Kafar labaran ta rika sukar shugaban kasar Rodrigo Duterte har
ta kai tana binciken sahihancin kalaman da yake yi a bainar
jama'a game da yaki da miyagun kwayoyi.
Watanni bayan da aka zabe shi a 2016, Rappler ta wallafa wani
cikakken rahoto kan yadda aka rika amfani da na'ura mai
kwakwalwa da shafukan sada zumunta na Facebook na bogi
wajen watsa sakonnin da ke zuzuta yawan goyon bayan da
shugaban ke da shi.

Daga nan Mista Duterte ya fara sukan shafin watsa labaran,
inda ya kira shi karkatacce har ya hana mai aika rahotanni
daga jaridar aiki a fadar shugaban kasa.
A watan Janairun bana hukumomin kasar suka kwace lasisin
da aka ba Rappler, matakin da ya janyo kace-nace daga
al'ummar kasar kan 'yancin aikin jarida.
A watan nan na Nuwamba kuma aka tuhumi Maria Ressa da
jaridar ta da kin biyan haraji - matakin da ta musanta.

Wa Lone da Kyaw Soe Oo

'Yan jaridar kamfanin dillancin labarai na Reuters Wa Lone da
Kyaw Soe Oo 'yan kasar Myanmar ne, kuma an daure su a
kurkuku na tsawon shekara bakwai a watan satumbar da ya
gabata saboda wai sun bayyana labaran sirrin gwamnatin
kasar.
Wannan ya biyo bayan wani aiki da suka yi ne a watan
satumbar 2017 na binciken kisan da sojin Myanmar su ka yi na
wasu 'yan kabilar Rohingya su 10 a kauyen Inn Dinn da ke
yankin Rakhine.
Daga nan aka kama 'yan jaridar su biyu a Disambar 2017 yayin
da suke dauke da wasu takardun gwamnati da wasu 'yan sanda
biyu suka basu.
Sun musanta aikata wani laifi, inda suke cewa 'yan sandan
kasar ne suka yi masu cinne.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.