Labaran duniya::: An harbe dan bindigar da ya kai hari kasuwar Faransa - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran duniya::: An harbe dan bindigar da ya kai hari kasuwar Faransa

<
Ministan cikin gidan Faransa ya ce 'yan sandan kasar sun
harbe har lahira mutumin da ya kai hari kan wata kasuwar
Kirsimeti da ke Strasbourg ranar Talata.
'Yan sandan sun gano dan bindigar mai suna Cherif Chekatt a
kan titin Strasbourg sannan suka harbe shi bayan ya bude wuta
da bindigarsa.
Mutum uku sun mutu bayan harbin da ya yi a kasuwar sannan
mutane da dama sun jikkata.
Chekatt, dan shekara 29, yana da tarihin aikata laifuka a
Faransa da Jamus sannan yana da'awar kaifin kishin addinin
Musulunci lokacin da yake daure a gidan yari. Ministan cikin gida Christophe Castaner ya ce 'yan sanda uku
ne suka hango wani mutum da ke da siffofi irin na Chekatt a
Neudorf kusa da Strasbourg da misalin karfe tara na dare a
agogon kasar.
Lokacin da suka tunkare shi domin tsayar da shi sai ya bude
musu wuta. Daga nan ne suka harbe shi, in ji Mr Castaner.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya gode wa jami'an
tsaro a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter sannan ya
sha alwashin zage damtse wurin "kawar da ta'addanci
dungurungum."
Daruruwan 'yan sandan Faransa da jami'an tsaro ne suka
kwashe tsawon lokaci suna neman Chekatt.
An kaddamar da gagarumin shirin neman sa a kusa da Neudorf
ranar Alhamis da safe, sai dai ba a gan shi ba.
An kama mutum biyar bisa zargin hannu a kai harin. Cikin su
har da iyayen Cherif Chekatt da 'yan uwansa biyu.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.