Labaran duniya::::: An gano kabarin wani malami na zamanin 'fir'auna' - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran duniya::::: An gano kabarin wani malami na zamanin 'fir'auna'

< Masar ta gano hubbaren wani babban jagoran addinin wanda
ya kai shekaru kusan dubu hudu da dari biyar da mutuwa.
An dai gano hubbaren ne a daya daga cikin katafaren yankin
Saqqara da ake da dalar Masar irin ta zamanin da.
Ma'aikatar adana kayayyakin tarihi ta masar ta ce hubbaren na
wani babban malamin addini ne na gidan sarauta da iyalansa a
lokacin daula ta biyar ta mulkin fir'aunan.
Bangon hubbaren na dauke da zane mutum-mutumin mutanen
gidan da kuma wasu zane-zane na kawa da ke nuna irin wasu
ayyukan da sukeyi kamar tuka jirgin ruwa, farautar tsunbtsaye
da hadaya.
Sakatare janar na majalisar koli da ke kula da kayyakin tarihi na
kasar ta Masar, Dokta Mostafa Al-Waziri, ya ce a hubbaren
akwai wasu sako-sako wanda ke nuna cewa akwai alamomin
wasu tarin kayayanki tarihi adane acikinsa.
A wannan lahadin dai ake shirin soma aikin tono hubbaren
wanda ake saran a sake gano wasu abubuwa tarihi da dama a ciki.G

Ga abubuwan da aka gano

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.