Labaran Duniya :: An Fatattaki 'Yan ISIS Daga Wani Muhimmin Wuri A Syria - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran Duniya :: An Fatattaki 'Yan ISIS Daga Wani Muhimmin Wuri A Syria

<
 — 
Wata kungiyar rajin kare hakkin bil adama a Syria ta ce, dakarun Syria masu samun goyon bayan Amurka, sun kwato wani muhimmin gari, wanda daya ne daga cikin wasu yankunan kasar Syria da su ka rage a hannun ISIS.
Kungiyar ta kula da hakkin bil adama a Syria ta ce “bayan wani mummunan fada na tsawon mako guda da ya hada da hare-haren jiragen sama, Dakarun rajin tabbatar da dimokaradiyya a Syria (SDF, a takaice), sun yi nasarar fatattakar kungiyar ISIS daga Hajin." Hajin dai, na lardin Deir Ezzor ne, mai tazarar kilomita 30 daga kan iyakar Syria da Iraki.
Mayaka wajen 17 na gamayyar Kurdawa da Larabawa da kuma dakarun SDF sun hada hannu wajen fatattakar 'yan ISIS daga yankin da ya rage a hannunsu a Syria, a cewar Abdel Rahman, shugaban kungiyar ta rajin kare hakkin dan adam a Syria.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.