Labaran duniya:::::: An ci gaba da lugudan wuta a Yemen duk da yarjejeniya - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran duniya:::::: An ci gaba da lugudan wuta a Yemen duk da yarjejeniya

<
Duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da a ka cimma kwanan
nan, rahotanni sun ce an ci gaba da lugudan wuta ta sama,
tare da bata-kashi a garin Hodeidah mai tashar jiragen ruwa
na Yemen.
Ana bata-kashin ne tsakanin dakarun gwamnati da 'yan
tawayen Houthi.
Majiyoyin gwamnati sun ce an kashe akalla mayaka ashirin da
tara a daren Asabar, akasarinsu 'yan tawayen Houthi.
Jami'ar bayar da agajin jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya a
Yemen, Lisa Grande ta shaidawa manema labarai cewa har yanzu ta na da
kyakkyawar fata, yarjejeniyar tsagaita bude wutar da aka
cimma a Sweden za ta yi tasiri.
Mataimakin ministan yada labarai na 'yan tawayen Houthi ya
ce yarjejeniyar za ta fara aiki daga ranar Laraba.
Duk kan bangarorin dake fadan za su janye mayakansu a cikin
'yan kwanaki da fara aiki da yarjejeniyar.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.