Thursday, 27 December 2018

Labaran chikin kasa Nigeria ::: Tsagerun Neja Delta sun ayyana sabuwar barazana game da zabukan 2019

Tags

Wata sabuwar kungiyar tsagerun Neja Delta dake ikirarin rajin kare hakkoki da kuma muradun yankin mai arzikin man fetur mai suna War Against Niger Delta Exploitation a turance sun ayyana barazanar kawo kancal ga zabukan 2019 masu zuwa.
Kungiyar dai ta bayyana cewa a shirye take ta hargitsa dukkan shirin gwamnatin tarayya na yin zabe a yankunan su idan dai har ba'a zauna an tattauna da su ba tare da magance masu matsalolin su da suka ce sun addabe su.
Wata sabuwa: Tsagerun Neja Delta sun ayyana sabuwar barazana game da zabukan 2019
Wata sabuwa: Tsagerun Neja Delta sun ayyana sabuwar barazana game da zabukan 2019
Legit.ng Hausa ta samu cewa kakakin kungiyar tsagerun mai inkiya da sunan ‘General’ Nomukeme shine ya sanar da hakan a cikin wata takardar manema labarai da ya rarraba a garin Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.
A cewar sa, kamar yadda muka samu a takardar, dole ne shugaba Buhari da kuma gwamnatin tarayya ta nuna masu ta damu da su ta hanyar kulawa da matsalolin su idan dai har ana so a yi zaben na 2019 cikin lumana kamar yadda ake ta tsare-tsare idan kuma ba haka ba kowa yaji a jikin sa.


EmoticonEmoticon