Labaran chikin kasa Nigeria :::: Hukumar Hisbah a Kano ta lalata manyan tireloli 30 da aka cika da barasa - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran chikin kasa Nigeria :::: Hukumar Hisbah a Kano ta lalata manyan tireloli 30 da aka cika da barasa

<
Hukumar Hisbah reshen jihar Kano ta kwace sannan ta lalata sama da tireloli 30 da aka cika da barasa
- Kakakin hukumar ya bayyana cewa an lalata kwalayen barasa a yammacin ranar Litinin bayan an kama su a Kalebawa a hanyar Danbata da ke yankin Dawakin Tofa
- Dokar jihar Kano dai ta haramta amfani da kayan maye a jihar
Hukumar Hisbah reshen jihar Kano ta kwace sannan ta lalata sama da tireloli 30 da aka cika da barasa.
Kakakin hukumar, Malam Adamu Yahaya, ya bayyana hakan a wata sanarwa a Kano a ranar Talata, 25 ga watan Disamba.
Hukumar Hisbah a Kano ta lalata manyan tireloli 30 da aka cika da barasa
Hukumar Hisbah a Kano ta lalata manyan tireloli 30 da aka cika da barasa
Yahaya ya bayyana cewa an lalata kwalayen barasa a yammacin ranar Litinin bayan an kama su a Kalebawa a hanyar Danbata da ke yankin Dawakin Tofa.
“Dokar jihar Kano lamba 4 na 200 ta haramta yin amfani da kayan maye a jihar.
“Don haka akwai wani umurni da kotun majistare ta bamu na aiwatar da shirin,” cewar shi.
Yahaya ya gargadi masu siyar da barasa da kada su wuce gona da iri.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.