Labaran chikin kasa Nigeria. :: Buhari ya gabatar da kasafin kudin 2019 na N8.83tr - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran chikin kasa Nigeria. :: Buhari ya gabatar da kasafin kudin 2019 na N8.83tr

<
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin kasar da ya kai naira tiriliyan 8.83 ga majalisar dokokin kasar.
An tsara kasafin ne bisa hasashen Najeriya za ta fitar da gangar mai miliyan biyu da dubu dari uku a ko wace rana.
Kuma an tsara kasafin ne bisa hasashen farashin danyen mai kan dala $60 kan ko wace ganga. Kuma kan farashin canji N305 kan dala daya.
Shugaba Muhammadu Buhari ya sha tafi da ihu a majalisa, yayin da yake jawabi kafin gabatar da kasafin kudi na shekarar 2019.
Shugaban ya ce wannan shi ne jawabin gabatar da kasafin kudi na karshe a majalisar dokokin kasa ta takwas. Wannan ne kuma kasafi na karshe da shugaban ya gabatar a wa'adin mulkinsa na farko da ke karewa.
A jawabinsa, Shugaba Buhari ya ce Najeriya ta fita daga koma-bayan tattalin arziki, sannan an samu raguwar hauhawan farashin kayayyaki, lamarin da ya janyo ma sa sowa da ihu daga bangaren 'yan adawa a zauren majalisar.
An ji wasu suna cewa "Karya ne," yayin da Buhari ke bayyana nasarorin gwamnatinsa. Wasu 'yan majalisar kuma sun ta yi masa tafi domin karfafa masa guiwa.
Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta yi aiki da yawa duk da ba ta samu kudi da yawa ba, a fannin noma da ayyuka da lantarki da kuma raya al'umma. Kuma ya ce a kowace jiha akwai aikin hanyoyi da gwamnatinsa ke yi.
Kuma ya ce gwamnatinsa ta yi kokari wajen taimakawa jihohi da tallafi domin biyan albashi da kudaden 'yan fansho.
Sai dai ya ce a kasafin kudin na 2019, akwai triliyan 2.14 da aka ware domin biyan bashi.
Kasafin na badi ya zarce na bara inda shugaban ya ce gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali wajen kammala ayyukan hanyoyi da wasu na ci gaba da aka soma.
Jawabin Buhari a takaice
Najeriya ta fita daga matsalolin koma-bayan tattalin arziki
Hauhawan farashin kayayyaki ya ragu daga kashi 18.17 a Janairun 2017 zuwa kashi 11.28 a Nuwamban bana
Kudin ajiyarmu ya karu daga dala bilian $28.57 a Mayun 2015 zuwa dala biliyan $42.92 a tsakiyar Disemban 2018.
Mun yi kokari wajen magance matsalar tsaro a arewa maso gabas da rikicin kabilanci a wasu wurare
Mun samu nasara a yaki da cin hanci da rashawa
Mun hana shigo da shinkafa daga waje
Mun samu ci gaba sosai wajen ayyukan ci gaba
Mun yi kokarin kammala ayyukan da muka samu maimakon kirkirar wasu sabbi
A 2018 an yi aikin hanyoyi na nisan kilomita 1,531, an yi wa wasu kwaskwarima na nisan kilomita 1,008 a sassan Najeriya
Abin da kasafin 2019 ya kunsa
Kasafin na Najeriya ya dogara ne da kudaden da kasar za ta samu daga albarkatun mai.
Game da wannan ne, Shugaba Buhari ya ce ya umurci kamfanin main a kasar NNPC ya dauki dukkanin matakan da suka dace domin tabbatar da samun cimma burin fitar da gangar mai miliyan biyu da dubu dari uku a kowace rana.
Shugaban ya ce kasafin kudin na 2019 na Naira tiriliyan 8.83 ya kunshi kudaden tallafi da kasar za ta samu biliyan N209.92.
Ma'aikatar cikin gida ce ta fi samun kaso mai yawa a kasafin kudin 2019 inda aka ware mata biliyan N569.07.
Ma'aikatar tsaro ce ta biyu, inda aka ware mata naira biliyan N435.62. Sai ma'aikatar ilimi da aka ware wa biliyan N462.24.
Ma'aikatar lafiya kuma an ware mata kudi ne naira biliyan N315.62.
An ware naira biliyan 45 ga shirin tallafawa yankin arewa maso gabas mai fama da rikicin Boko Haram da kuma naira biliyan 10 ga sabuwar hukumar raya yankin.
Haka kuma shugaba Buhari ya ce domin ci gaba da tabbatar da zaman lafiya a yankin Neja an sake ware wa shirin afuwa na yankin naira biliyan 65 a kasafin na 2019.
Kasafin kudin dai zai zama doka ne kawai idan 'yan majalisar kasar suka amince da shi.
An dade ana jiran gabatar da kasafin kudin 2019 a majalisa, yayin da babban zabe a kasar ke karatowa.
Wasu na ganin kamar an makara domin ba majalisa damar fara nazari har a kai ga amince wa da shi yayin da ya rage watanni a gudanar da babban zabe a Najeriya.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.