Bollywood ::::: Kun san jaruman Indiya marassa galihun da suka yi fice? - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Bollywood ::::: Kun san jaruman Indiya marassa galihun da suka yi fice?

<
 1.Amitabh Bachchan
Amitabh Bachchan, na daya daga cikin jaruman Indiyan da
suka yi fice ba kasarsu ba kadai, har ma a sauran kasashen
duniya.
Da farkon dai a rayuwarsa ya so ya zamo mai aiki a gidan
rediyo, irn masu gabatar da shirye-shiryen nan, to amma a
lokacin da ya je wani gidan rediyo domin aiki sai aka ki
daukarsa saboda babbar muryar da ya ke da ita.
Amitabh Bachchan, saboda tsabar neman abinyi a lokacin,
yakasance har kwana ya ke a benci a wajen da ya kanje neman
aiki.
Haka ya yi ta gwagwarmaya, har da karshe ya samu da kyar
aka gwada shi yin fim.

a farko andan aka gwada shi, sai aga ba zai iya ba, a haka dai
har ya samu aka saka shi a cikin fim.
A yau, Amitabh, na daga cikin masu kudin Indiya ma, ba wai a
bangaren jarumai ba kawai.
2.Mithun Chakraborty
Mithun Chakraborty wanda jama'a da dama suka fi saninsa da
sarkin rawa, shi ma ya yi gwagwarmaya a rayuwarsa kafin ya
zama wani.
Mithun yakasance a wasu lokuta har kwana ya ke da yunwa
saboda tsananin ba bu.
Da farko rayuwarsa ba yabo ba fallasa, amma bayan rasuwar
wani wansa kwalli daya tal, sai rayuwarsa ta sauya.
Ya sha matukar wuya wajen fadi tashin neman abin yi, amma
daga bisani hakarsa ta cimma ruwa da ya ke yana da wasu
abubuwa da za su sa a sanya shi a fim, ciki kuwa har da rawa.
Yanzu yana daga cikin jaruman Indiyan da suka yi fice sosai,
kuma ya tara abin hannunsa.
3.Shah Rukh Khan
Jarumin da ake yayinsa wanda aka yi wa lakabi da "Badshah
na Bollywood".
To amma kafin ya kai matsayin da ya kai a yanzu, shi ba wani
bane.
Bayan ya yi karatunsa, sai ya je ya fara aiki a wani wurin cin
abinci, daga baya ya bude na sa wajen cin abincin, amma daga
bisani jarinsa ya karye.
Sai ya koma wani wajen siyar da abincin ya ke aiki cikin masu
raba abincin a Delhi.
Albashinsa a lokacin, bai taka kara ya karya ba, amma duk da
haka a kullum cikin burin ganin ya zama wani ya ke.
Haka ya yi tayin gwagwarmaya, har Allah ya kai shi matsayinsa
na yanzu, inda a cikin jaruman fina-finan Indiyan ma yana daga
gaba-gaba a jerin masu kudi.
Ya samu karbuwa sosai a wajen jama'a.
4.Akshay Kumar
Akshay Kumar, shima fitaccen jarumi ne a fina-finan Indiya,
wanda a yanzu haka ma yana daga cikin jarumai maza da suke
cajar kudi mai yawa a fim.
Kafin ya fara fim, ya fara aiki ne a matsayin mai dafa abinci a
otel d akuma raba abincin ga bakin da suka je otel din a
Bangkok.
Ya kan kuma sayar da kayan d aya ke sayowa daga Bangkok
idan ya je Indiya hutu.
Daga nan kuma sai ya koma taimakawa wani abokinsa sayar
da gidaje da fulotai, anan ne ma ya dan samu abin kansa.
Amma a yau, sai dai ya bayar da gida, saboda daukakar da
Allah ya yi masa, da kuma makudan kudin da ya ke da su ta
hanyar sana'ar fim.
5.Dilip Kumar
Tsoho mai ran karfe ke nan, wanda ya bar babban tarihi a fina-
finan Indiya.
Dilip Kumar ya fuskanci kalubale kala-kala a rayuwarsa da
farko.
Jarumin kafin ya fara fim har duniya ta san shi, ya yi
gwagwarmayar neman kudi, domin kuwa har sana'ar sayar da
kayan marmari ya yi.
Da ya dan tara 'yan kudadensa, sai ya je ya bude wani dan
karamin shagon sayar da kayayyaki.
A haka- a haka, hat ya samu wani abokinsa wanda babban dan
siyasa ne a wancan lokaci ya taimaka shi da kudi ya je domin
ya shiga fim.
Ya yi sa'a kuma aka zabe shi. daga nan ne kuma al'amura
suka fara canzawa.
Duk da ya ke yanzu ya tsufa sosai har ya daina fim,
masana'antar fina-finai ta Bollywood ba za ta taba mantawa
da irin gudunmuwar da bayar ba a lokacin da ya ke fim.
Ba a samu jarumin da har yanzu ya kama kafarsa wajen farin
jini da iya fim da kuma samun lambobin yabo ba.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.