Zaman takewa ::: Adikon Zamani: Batun Sadakin Aure Kashi na 2 - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Zaman takewa ::: Adikon Zamani: Batun Sadakin Aure Kashi na 2

<
Wannan ne kashi na biyu na shirin Adikon Zamani a kan batun
sadakin aure wanda ke daga cikin abubuwan da kan janyo
takardama tsakanin al'umma.
A matsayinsa na daya daga cikin ginshikan aure da Musulunci
ya tanadar, muhimmancin sadaki ba ya misaltuwa.
Amma kamar yadda dukkan al'amarin dan Adam, an mayar da
batun abu mai sarkakiya da wahalaswa har ya kai ga mutane
ba sa iya gane ainihin dalilin da aka sanya shi tun da farko.
Daya daga cikin abubuwan da kan dami al'umma game da
batun sadaki shi ne wani sabon salo da mazaje masu neman
aure kan mika sadaki ga iyalan matar da za a aura tun kafin a
daura auren.
Saboda wannan, sai kaga mutumin yana dora wa matar wasu
bukatu wadanda na ma'aurata ne kawai, kuma wannan
halayyar sai kara yawa ta ke yi.
Ta yaya lamarin ya kai ga wannan matakin? Yaya za mu iya
dakatar da shi zama al'ada ta karfi da yaji?
A wanna makon mun tattauna da wasu mata da fitattun
masana ilimin addinin Islama ne domin sanin ainihin yadda ya
kamata a rika bayar da sadakin aure.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.