Monday, 31 December 2018

Technology :::An Introduction to Chaos Theory with the Lorenz Attractor

Labaran Duniya :: Janye Sojojin Amurka Daga Syria Babbar Barazana Ce Ga Israi'la

Tags
Biyo bayan ganawaa da sanata Linsey Graham yayi da Shugaba Donald Trump, ya ce yana da kwarin gwiwa cewa zai dakatar da aniyarsa ta janye sojojin Amurka daga Syria, wanda hakan zai baiwa Iran damar ci gaba da yiwa Isra'ila Barazana.

Islamic ::: Kungiyar Ahmadiyya Tayi Taron Shekara A Jamhuriyar Nijar

Tags

Kungiyar Ahmadiyya Tayi Taron Shekara A Jamhuriyar Nijar

Taron Kungiyar Ahmadiyya a Jamhuriyar NijarPhoto: Harouna Kungiyar Ahmadiyya wacce ta samo asali daga kasar Pakistan, yanzu haka ta samu karbuwa a fadin Jamhuriyar Nijar, inda tayi taron ta na shekara da ake kira Jalsa Salana da aka bude shi jiya a birnin Konni.

Zaman takewa :: Taron Kabilar Kambari Ya Ja Hankali Kan Zaben Kasa


Taron Kabilar Kambari Ya Ja Hankali Kan Zaben Kasa

Taron Shekara 2018 Na Kabilar Kambari Photo: Mustapha Nasiru Batsari (VOA)

A kalla 'yan kabilar Kambari dubu biyar ne suka halarci taron su na wannnan shekarar, duk da matasalar da yankin nasu yake fama da shi na rashin hanyar motada sauran ababan more rayuwa.

Labaran chikin kasa Nigeria ::: Mayakan Saman Najeriya Sun Rugurguza Sansanin Yan Bindigar Zamfara

Tags
Rundunar Sojan saman Najeriya ta kaddamar da tashin jiragenta a filin jirgin saman Sultan Abubakar don tunkarar 'yan bindiga a yankunan jihohin Sokoto da Kebbi, inda ta kara karfin sansaninta na runduna ta 119 dake Jihar Sokoto.

Saturday, 29 December 2018

Labaran wasanni::::::: Modric ya lashe kyautar gwarzon Balkan

Tags
Dan wasan Real Madrid, Luka Modric ya lashe kyautar
gwarzon dan wasan kudu maso yammacin Turai na shekarar
2018, wato Balkan Athlete of the year.

Modric dan kasar Croatia shi ne dan kwallon kafa na biyu da
ya ci kyautar, bayan Hristo Stoichkov gwarzon dan kwallon
kafar nahiyar Turai a shekarar 1994.

Dan wasan mai shekara 33 ya yi nasara ne da maki 77 a biki
na 46 da kamfanin yada labarai na Bulgaria (BTA) kan
gudanar, ya kuma doke Novak Djokovic wanda ya jera karo
biyar yana lashe kyautar tun daga 2011 zuwa 2015.

Modric shi ne ya lashe kyautar Ballon d'Or ya kuma ci kofin
Zakarun Turai da na Zakarun nahiyoyin duniya da Real Madrid,
ya kuma kai Croatia wasan karshe a kofin duniya shi ne
gwarzon gasar a Rasha.

Labaran wasanni::::: 'Liverpool za ta lashe Premier ba a doke ta ba'

Tags
Kocin Arsenal, Unai Emery ya ce Liverpool za ta bi sawun
Gunners na lashe kofin Premier ba tare da an doke ta ba a
kakar shekarar nan.


Arsenal za ta ziyarci Anfield a ranar Asabar a gasar Premier
wasan mako na 20, Liverpool tana ta daya a kan teburin da
tazarar maki shida, kuma har yanzu babu kungiyar da ta doke
ta a bana.


Liverpool ta yi nasarar cin wasa takwas a jere tun 2-2 da ta yi
da Arsenal a Emirates a ranar 3 ga watan Nuwamba.
Arsenal ce a cikin karnin nan ta lashe kofin Premier ba tare da
an doke ta ba a kakar 2004, karkashin Arsene Wenger.
Emery ya ce yana ganin Liverpool za ta iya lashe Premier
shekarar nan ba tare da an doke ta ba, domin tana da 'yan
wasan da za su kai kungiyar ga yin nasara.

Zaman takewa ::: Adikon Zamani: Batun Sadakin Aure Kashi na 2

Wannan ne kashi na biyu na shirin Adikon Zamani a kan batun
sadakin aure wanda ke daga cikin abubuwan da kan janyo
takardama tsakanin al'umma.
A matsayinsa na daya daga cikin ginshikan aure da Musulunci
ya tanadar, muhimmancin sadaki ba ya misaltuwa.
Amma kamar yadda dukkan al'amarin dan Adam, an mayar da
batun abu mai sarkakiya da wahalaswa har ya kai ga mutane
ba sa iya gane ainihin dalilin da aka sanya shi tun da farko.
Daya daga cikin abubuwan da kan dami al'umma game da
batun sadaki shi ne wani sabon salo da mazaje masu neman
aure kan mika sadaki ga iyalan matar da za a aura tun kafin a
daura auren.
Saboda wannan, sai kaga mutumin yana dora wa matar wasu
bukatu wadanda na ma'aurata ne kawai, kuma wannan
halayyar sai kara yawa ta ke yi.
Ta yaya lamarin ya kai ga wannan matakin? Yaya za mu iya
dakatar da shi zama al'ada ta karfi da yaji?
A wanna makon mun tattauna da wasu mata da fitattun
masana ilimin addinin Islama ne domin sanin ainihin yadda ya
kamata a rika bayar da sadakin aure.

Zaman takewa ::: Adikon Zamani Batun Sadakin Aure

Al'amarin aure a kowane bangare na duniya babban al'amari
ne, kuma batun sadaki na daga cikin abubuwan da kan janyo
takardama tsakanin al'umma.
A matsayinsa na daya daga cikin ginshikan aure da Musulunci
ya tanadar, muhimmancinsa ba ya misaltuwa.
Amma kamar yadda dukkan al'amarin dan Adam, an mayar da
batun abu mai sarkakiya da wahalaswa har ya kai ga mutane
ba sa iya gane ainihin dalilin da aka sanya shi tun da farko.
Daya daga cikin abubuwan da kan dami al'umma game da
batun sadaki shi ne wani sabon salo da mazaje masu neman
aure kan mika sadaki ga iyalan matar da za a aura tun kafin a
daura auren.
Saboda wannan, sai kaga mutumin yana dora wa matar wasu
bukatu wadanda na ma'aurata ne kawai, kuma wannan
halayyar sai kara yawa ta ke yi.
Ta yaya lamarin ya kai ga wannan matakin? Yaya za mu iya
dakatar da shi zama al'ada ta karfi da yaji?
A wanna makon mun tattauna da wasu mata da fitattun
masana ilimin addinin Islama ne domin sanin ainihin yadda ya
kamata a rika bayar da sadakin aure.

Labaran siyasar chikin kasa Nigeria :: wai Maine gaskia labarineBa gaskiya bane cewar Dangote na cikin kungiyar yakin zaben Buhari - Fadar shugaban kasa shine da gaske ko yaya ?

Tags
Fadar shugaban kasa, ta fito ta karyata wani rahoto da Femi Adesina ya fitar, na cewar Aliko Dangote na daga cikin mambobin kwamitin yakin zaben Buhari
- Fadar shugaban kasar ta ce akwai muhimmancin fayyacewa 'yan Nigeria gaskiya kan matsayar Dangote a cikin harkokin kwamitin yakin zaben shugaban kasar
- Haka zaika, fadar shugaban kasar ta ce Dangote bai da katin shaidar zama dan jam'iyyar APC, don haka ba zai taba zama mamba na wannan kwamiti na PCC ba
Bayan sanya sunan hamshakin dan kasuwa, kuwa wanda yafi kowa kudi a Afrika, Aliko Dangote, a cikin mambobin kwamitin mashawarta na yakin zaben shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC, fadar shugaban kasa yanzu ta ce Dangote baya daga cikin mambobin wannan kwamiti.
A cikin wata sanarwa kan batun kafa kwamitin wada Femi Adesina ya rabawa manema labarai a ranar Juma'a, ya sanya sunan Atiku a cikin jerin sunayen mambobin kwamitin wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ke a matsayin shugaba, yayin da Asiwaju Bola Tinubum Sanata Ahmed Lawan (shugaban masu rinjaye a majalisar dattijai), Hon Femi Gbajabiamila (shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan tarayya) da kuma shugaban APC na kasa, Adams Oshiomole a matsayin mambobi.
Ba gaskiya bane cewar Dangote na cikin kungiyar yakin zaben Buhari - Fadar shugaban kasa
Ba gaskiya bane cewar Dangote na cikin kungiyar yakin zaben Buhari - Fadar shugaban kasa
Sai dai a cikin wata sanarwa daga kakakin fadar shugaban kasa, da ya rabawa manema labarai a daren ranar Juma'a, na cewa: "Hakika zai zama abu mai matukar muhimmanci, wayar da kan jama'a dangane da sanya sunan Alhaji Aliko Dangote, a cikin mambobin kwmaitin mashawarta na kungiyar yakin zaben shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC, kamar yadda wata sanarwa ta gabata a ranar Juma'a 28 ga watan Disambar 2018.
"Wanda yafi kowa kudi a Afrika, baya daga cikin mamallaka katin shaidar zama dan jam'iyyar APC, don haka ba zai taba zama mamba na wannan kwamiti na PCC ba. Haka zalika bashi daga cikin mambobin kwamitin zaman lafiya na jam'iyyar, don haka, ba zai iya tsoma hannunsa a cikin harkokij yakin zaben kwamitin da jam'iyyar ba."

Labaran Duniya ::: Maine gaskia labarin Amurka Ta Karyata Batun Kwace Birnin Manbij Da Syria Tace Ta Yi

Tags
Duk da ikirarin da rundunar yankin Manbij ke yi cewa ta kwace ikon yankin, sakamon gagarumin janyewar sojojin Amurka a Syria, jami’an sojin Amurka sun ce ya zuwa yanzu babu wani abin da ya canza a wurin.
Amurka a jiya Juma’a ta yi watsi da batun soijojin Syria sun kwace ikon birnin Manbij dake arewa maso gabashin Syria, inda ake bata kashi tsakanin mayakan Kurdawa masu samun goyon bayan Amurka da sojojin Turkiya, bisa bukatar Kurdawan Syria.
A cikin wata sanarwa, ma’aikatar sojin Syria tace dakarunta sun kwace muhimman wurare kuma ta kara da tabbatarwa al’ummar yankin cewa akwai cikakken tsaro ga ‘yan Syria da ma wasu dake zaune wurin.
Sai dai rundunar hadin gwiwa a jagorancin Amurka dake yaki da kungiyar IS a wurin ta maida martani ta sakon Twitter tana fadar cewa babu alamar gaskiya a wannan maganar.
Kana rundunar hadin gwiwar ta kara da yin kira ga duk wani mahaluki da ya mutunta ‘yancin Manbij da kuma tsaron mutaneta

Labaran Duniya :: Trump Yana Shirin Rufe Iyakar Amurka Da Mexico

Tags

A cikin wasu jerin sakwannin Twitter, Trump ya yi kira da a canja dokar bakin hauren kasar, wanda ya kira da abar kunya.
Kalaman na shi suna zuwa ne yayain da rufe wani bangaren gwamnatin Amurka ke shiga kwana na cikon bakwai sakamakon rashin amincewa da bukatar Trump a kan kasasfin kudin kasar, inda ya bukaci dala biliyon biyar domin gina Katanga, lamarin da ‘yan majalisa na Democrats suka bada shawara kara karafafa tsaron kan iyakar baki daya amma suka kalubaknci gina katangar.
Rufe iyakar Amurka da Mexico dai yana nufin za a samu tsaiko a kan huldar kasashen biyu wanda ke haifar da cinikin dala biliyon daya da miliyon dari shida da tamanin a duk rana ta Allah.

Labaran Najeriya:::: Buhari ya kaddamar da yakin neman zabe

Tags
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da yakin
neman zabensa a garin Uyo dake jihar Akwa Ibom.
Shugaban ya yi jawabi ga tarin mutanen da suka hallara a filin
wasa na garin.
Buhari ya yi bayani kan tsaro inda ya tabbatar da cewa
kungiyar Boko Haram bata rike da gari ko daya a halin yanzu a
Najeriya, don haka gwamnatinsa ta yi nasara a kan kungiyar.
Shugaban ya bayyana cewa a lokacin da ya karbi mulki a 2015,
Boko Haram na rike da kananan hukomi kusan 17 a jihohin
Barno da Yobe, amma a halin yanzu ba ta da iko da ko daya.
Ya ce gwamnatinsa za ta cigaba da tabbatar da tsaro da
habbaka tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

Shugaban ya bayyana cewa an kwato kadarori da kuma kudade
a yaki da ake yi da cin hanci da rashawa.
A bangaren tattalin arziki, ya bayyana cewa an samu ci gaba
wajen samar da abinci a Najeriya ta hanyar inganta noma da
kuma hana fasa kwaurin shinkafa.
Sai dai ya bayyana rashin aikin yi a matsayin matsala a kasar
ganin cewa kashi 60 cikin 100 na 'yan kasar matasa ne.
Tsohon gwamnan jihar ta Akwa Ibom Sanata Godswill Akbabio
shi ne shugaban yakin neman zaben na Shugaba Buhari.
Hakan ne ma ya sa ake ganin cewa an zabi jihar ta Akwa ibom
ta zama jihar da za'a kaddamar da yakin neman zaben.
Duk da cewa jamiyyar adawa ta PDP ce ke da iko a jihar,
Sanata Akpbabio dan siyasa ne mai karfin fada a ji wanda
kuma yake da tasiri a harkokin siyasar jihar.
Wannan dai shi ne yakin neman zabe karo na 5 da Shugaba
Muhammadu Buhari zai yi a Najeriya.
A 2003 ya yi yakin neman zabe tare da Chuba Okadibo a
matsayin mataimakin sa.
Haka a 2007 ya yi yakin neman zaben tare da Edwin Ume-
Ezeoke.
A 2011 ya fito tare da Tunde Bakare a matsayin mataimaki.
A zaben 2015 kuma tare da Farfesa Yemi Osibanjo wanda a
lokacin ne ya yi nasarar lashe zaben.
A yanzu, ya kara zabar Farfesa Yemi Osinbanjo a matsayin
mataimakinsa domin neman shugabancin kasar karo na biyu.
Mutane da dama suna jira su ga yadda wannan yakin neman
zaben na Shugaban Najeriya zai kasance.
Hakan ba ya rasa nasaba da cewa a 2014, akwai jiga-jigan 'yan
jam'iyyar ta Apc da dama wadanda aka zagaya dasu wajen
yakin neman zaben amma daga baya sun sauya sheka zuwa
wasu jam'iyyu.
Babban abin tambaya a nan shi ne, ko za'a samu taron mutane
kamar yadda aka samu a yakin neman zaben shekarar 2014
koko a'a?
Ana sa ran dai a wannan lokacin shugaban zai ci gaba da yakin
neman zaben ne akan samar da tsaro a kasar da kuma yaki da
cin hanci da rashawa da kuma kara habaka tattalin arzikin
kasar.
A kwanankin baya ne dai gwamnatin jihar ta Akwa Ibom ta fitar
da sanarwar cewa ba za ta yarda ayi amfani da filin wasa na
jihar ba domin gudanar da yakin neman zaben sakamakon
gasar kwallon Firimiya ta Najeriya da za'ayi a fili.
Daga baya ne dai gwamnatin jihar ta amince da ayi amfani ta
filin wasan domin kaddamar da yakin nemen zaben.

Labaran Najeriya::: Takaitaccen tarihin Alhaji Shehu Shagari

Tags
Mun sake wallafa muku wannan makala ne a karo na biyu
sakamakon rasuwar Alhaji Shehu Shagari. Mun fara wallafa ta a
ranar 16 ga Satumbar 2010.
An haifi Alhaji Shehu Shagari a kauyen Shagari a shekarar
1925, kuma shi ne da na shida ga mahaifinsa Aliyu, magajin
kauyen Shagari, wanda manomi ne, dan kasuwa yana kuma
kiwo.
Allah ya yi wa mahifinsa rasuwa yana dan shekara biyar da
haihuwa.
Alhaji Shehu Shagari ya fara karatun kur'ani tun yana dan
shekara hudu, kuma daga bisani ya je makarantar Elimentari
da ke garin Yabo kusa da kauyen Shagari, daga nan kuma ya
tafi makarantar Middle a Sokoto, daga nan kuma ya je kwaleji
ta Kaduna.
Bayan da ya kammala karatun sakandirensa, Alhaji Shehu
Shagari ya yi koyarwa a makarantun middle daban-daban a
matsayin malamin kimiyya da ma tarihi.
Tun yana kwaleji, Shagari ya fara nuna sha'awar shiga siyasa,
inda a shekarar 1946 shi da Malam Gambo Abuja suka kafa
wata kungiyar matasa a Sokoto, kuma sun samu goyan bayan
dattijai kamar Sir Ahmadu Bello da Ibrahim Gusau da kuma
Malam Ahmadu Dabbaba.
A shekarar 1948 ne kuma aka amince da a hade dukkanin
kungiyoyin siyasar yankin zuwa kungiyar NPC wadda daga
bisani ta zama jam'iyyar da ta tsaya takara a zaben shekarar
1959.
Kafin wannan shekarar ne aka zabi Shagari a matsayin wakilin
mazabar Kudu-maso Kudancin Sokoto, kuma a shekarar 1958,
an zabe shi a matsayin sakataren majalisar Firaminista, Sir
Abubakar Tafawa Balewa.
Daga bisani Shagari ya rike mukaman minista daban-daban da
suka hada da na ci gaban tattalin arziki (1960), da na kula da
harkokin cikin gida (1962) da kuma na ayyuka da safiyo (1965).
Bayan juyin mulkin farko da sojoji suka yi, Alhaji Shehu Shagari
ya koma gida Sokoto.
Da hawan janar Gowon ya bai wa Shagari ministan kula da
harkokin tattalin arziki, daga bisani kuma aka ba shi ministan
kudi.

Friday, 28 December 2018

Hollywood news. ::: Charges For Owning A Pet Monkey

Chris Brown May face 6months in jail for owning a Pet Monkey. While some people believe that a dog is a man’s best friend, others opt to buy monkeys. Although the exotic creatures can be purchased as pets in many countries, the laws in the United States require an owner to have a proper permit to own the animal. Chris Brown must have missed that part of his monkey manual though.
 Brown is in trouble with the law yet again. This time though, the charges stem from the talented singer’s pet monkey. As reported by TMZ, the Los Angeles City Attorney’s Office is charging Brown with two counts of owning a restricted species without a permit. The violations carry a maximum sentence of 6 months in jail. Brown brought home the baby capuchin monkey named Fiji and allowed his daughter to play with the pet on his social media. If you recall, that didn’t go over so well.
Brown was forced to give up the pet after a horde of people online reported him to the authorities. At the time, which was at the top of 2018, we reported that he would possibly get hit with criminal charges. Those charges have finally been filed. Brown is due in court on February 6, and hopefully, he’s only hit with a few fine

s

Hausa hip hop music ::: Delux – Nigga We Flow Ft. Sarkin Arewa

Music ::: YEESS BOSS NATION BOSS Just feature MGN BOSS Sarkin_arewa TITLE NIGGA_,we_FLOW DOWLOAD AND LISTEN YOUR LIKE IT JST HIT THE DOWLOADiNG BOTTOM AnD IS ALL YOUS         DOWNLOAD MUSIC HERE

Thursday, 27 December 2018

Labaran chikin kasa Nigeria ::: Shin Boko Haram ta kori sojoji ta kwace garin Baga?

Tags
Rahotanni daga Baga da ke jihar Barno a arewa maso gabashin Najeriya sun nuna cewa mayakan Boko Haram sun shiga garin inda suka kara da sojojin Najeriya.
Wasu bayanai na cewa mayakan sun kafa tuta a garin na Baga bayan sun shafe daren Laraba suna fafatwa da sojoji da ke garin.
Wani mazaunin gairn da ya shaida lamarin yace 'yan Boko Haram din sune ke iko da garin, domin sun kafa tuta, sannan babu wani soja ko da ya da ya rage a cikin garin.
Ya bayyana wa BBC cewa mayakan sun afkawa wani babban sansanin soji da ke gefen ruwa a garin na Baga.
'Yan Boko Haram sun kai hari garin Gudumbali na jihar Borno
An kama daya daga cikin shugabannin Boko Haram a Najeriya
Sojojin Najeriya sun dakile harin 'yan Boko Haram
To sai dai kakakin rundunar sojan kasa ta Najeriya Janar Sani Kukasheka Usman ya ce Boko Haram ba ta kwace garin ba, amma suna ci gaba da wani aiki a garin, kuma nan gaba za su yi karin bayani kan halin da ake ciki.
Rundunar sojin Najeriya dai ta sanar cewa mayakan Boko Haram sun kai hari shelkwatar dakarun gamayya na kasashen yankin tafkin Chadi ne da ke Baga a jiya Laraba.
Ta ce dakarunta sun yi fada kan jiki kan karfi don korar mayakan Boko haram din, kuma daya daga cikin sojojin ya rasa ransa a yayin fadan.
Sai dai wanda ya shaida lamarin ya ce mayakan sun shiga garin na Baga bayan wasu daga cikinsu sun yi wa sansanin sojojin kawanya.
Ya kuma ce sojojin da ke cikin garin Baga sun tsere zuwa Munguno.
Ya bayyana cewa mayakan sun kafa tutarsu a babban masallacin Juma'a na garin Baga, kuma 'yan bindigan ne ma suka ja sallar Asuba.
"Muna isa masallaci sai muka ga mutane rike da bindigogi", a cewarsa.
Ya ce 'yan bindigan sun yi wa jama'ar garin bayanin cewa su mayakan Boko Haram ne na bangaren Mamman Nur kuma babu ruwansu da dukiyar talaka ko kashe mutane.
"Sun ce su 'yan kungiyar IS ne, kuma sun ce mu kwantar da hankalinmu", in ji shi.
A halin yanzu dai, mutumin ya ce ya tsere Maiduguri kuma bai fuskanci wani tashin hankali ba daga gurin 'yan bindigan duk da cewa a idonsu ya fita ya bar garin.
Rundunar Sojin Najeriya dai ta ce mayakan Boko Haram din na buya a garin Baga da kewaye kuma dakarunta na kokarin gano su.
Rundunar ta kuma ce an tura karin sojojin ruwa da na kasa don samun karin karfin korar 'yan ta'addan.

Labaran Duniya. ::: Shugaban Amurka Donald Trump ya koma fadarsa a yau Alhamis bayan da ya kai wata ziyara ta ba-zata ga dakarun Amurka da aka girke a Iraqi.

Tags
Shugaban Amurka Donald Trump ya koma fadarsa a yau Alhamis bayan da ya kai wata ziyara ta ba-zata ga dakarun Amurka da aka girke a Iraqi.

Labaran Duniya ::: Yan Jaridar Sudan Sun Fara Yajin Aiki, Da Goyon Bayan 'Yan-Adawa

Tags
Wasu ‘yan jaridar kasar Sudan sun tsunduma cikin yajin aiki, don nuna goyon bayansu ga zanga-zangar adawa da gwamnatin shugaba Omar al-Bashir.

Labaran siyasa Nigeria :: Gwamnatin Jihar Taraba Ta Daga Darajar Masarautun Gargajiya

Tags
Kafin dai wannan bukin bada sandar girman, wasu sun kai hari fadar sarkin Kwajji dake garin Puppule, domin nuna adawarsu da nada sabon sarkin da aka yi, Alh. Umar Buba Nyala,wanda ya gaji sarautar daga mahaifinsa da ya rasu kwanakin baya.
Da yake jawabi yayin bada sandar girman, gwamnan jihar Taraban Akitek Darius Dickson Isiyaku, yace gwamnatinsa zata cigaba da marawa sarakunan gargajiya baya, domin kwalliya ta biya kudin sabulu, don wanzar da zaman lafiya a jihar, jihar dai na faman farfadowa daga tashe tashen hankula.
Gwamnan ya mika sandar girmar ga sabon sarkin kwajji Umar Buba Nyal,a da aka daga darajar masarautar daga daraja ta uku zuwa ta biyu, da kuma wasu daggatai da suka koma darajar hakimai masu daraja ta uku.
Shi kuwa da yake jawabi a madadin sarakunan da aka daga darajar tasu sarkin Jen Alh. Ismaila Agwaru, ya tabbatar cewar zasu cigaba da bada nasu gudumawa wajen cigaban jihar.
Wannan ranar farin ciki ne a gare mu, kuma zamu bada namu gudumawa a matsayin sarakuna, iyayen kasa, domin samun zaman lafiya. Zamu yi aiki tukuru bada nuna son kai ga wani ko wasu ba, domin a samu cigaba a masarautun mu da jihar Taraba dama kasa baki daya.
Sarakunan da aka daga darajar tasu sun ko hada dana kwajjin Umar Buba Nyala, da Enoch Tanko Tabena sarkin Ndola, da na Tigun Ibrahim Etsu da kuma na Ichen Kurmi Ismaila Maiwuya.

Music ::: Mariah Carey – All I Want for Christmas Is You

Tags
Music. :::

Mariah Carey All I Want for Christmas Is You

Mariah Carey’s Song ‘All I Want for Christmas Is You‘ Breaks The spotify record for the most streamed a day. According to Spotiy’s official charts, Mariah’s holiday song scored 10,819,009 streams on Christmas eve (Dec. 24th), breaking the earlier record held by XXXTentacion’s ‘SAD!’ — it earned 10.4 million Spotify streams on June 19th, 2018, one day after his death

If you have a look at the most streamed songs on Dec. 24th in the screenshot below, each one of them is Christmas themed. Mariah wrote and produced the song alongside Walter Afanasieff, releasing on November 1, 1994 as the lead single from her fourth studio album and first holiday album, Merry Christmas. ‘Thank U, Next’ had earlier broken Spotify’s global, single-day streaming record for a female artist on Nov. 5, earning nearly 8.2 million streams. Mariah has now broken both overall and female-specific records.

Audio PlayerDownload Mariah Carey All I Want for Christmas Is You Mp3
;
00:00
00:00

Naija Music ::: Mr Real Zzz ft Falz

Music. :: 

Mr Real Zzz

Mr Real wraps up the year 2018 with a new song ‘Zzz’ featuring Falz Produced by Cracker. It serves as his second release of the year, it comes after the visual to the remix of his chart-topping single ‘Legbegbe’.             DOWNLOAD MUSIC HERE

Hausa Hip Hop music ::: Dj Ab – Azuba Shi Ft. Kheengz

Music :::   Northern Nigerian lyrical titan DJ AB also known as the intelligentleman teams up with YFK finest, Kheengz on a joint labeled “Azuba shi” (DJ AB ft Kheengz).            DOWNLOAD MUSIC HERE

Labaran chikin kasa Nigeria ::: Tsagerun Neja Delta sun ayyana sabuwar barazana game da zabukan 2019

Tags
Wata sabuwar kungiyar tsagerun Neja Delta dake ikirarin rajin kare hakkoki da kuma muradun yankin mai arzikin man fetur mai suna War Against Niger Delta Exploitation a turance sun ayyana barazanar kawo kancal ga zabukan 2019 masu zuwa.
Kungiyar dai ta bayyana cewa a shirye take ta hargitsa dukkan shirin gwamnatin tarayya na yin zabe a yankunan su idan dai har ba'a zauna an tattauna da su ba tare da magance masu matsalolin su da suka ce sun addabe su.
Wata sabuwa: Tsagerun Neja Delta sun ayyana sabuwar barazana game da zabukan 2019
Wata sabuwa: Tsagerun Neja Delta sun ayyana sabuwar barazana game da zabukan 2019
Legit.ng Hausa ta samu cewa kakakin kungiyar tsagerun mai inkiya da sunan ‘General’ Nomukeme shine ya sanar da hakan a cikin wata takardar manema labarai da ya rarraba a garin Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.
A cewar sa, kamar yadda muka samu a takardar, dole ne shugaba Buhari da kuma gwamnatin tarayya ta nuna masu ta damu da su ta hanyar kulawa da matsalolin su idan dai har ana so a yi zaben na 2019 cikin lumana kamar yadda ake ta tsare-tsare idan kuma ba haka ba kowa yaji a jikin sa.

Labaran chikin kasa Nigeria ::: jiya ba yauba Yadda aka sa Buhari cikin mari yayin juyin mulkin da aka yi masa a 1985

Tags
Sabanin yadda ake yadawa a wurare da yawa cewa tsohon mai baiwa Shugaba Jonathan shawara akan harkokin tsaro, Kanal Sambo Dasukin yana cikin Sojojin da suka je suka kamo Shugaba Buhari a juyin mulkin 1985, gamasasshen bayani ya nuna cewa ba haka bane.
Kamar dai yadda muka samu daga wasu majiyoyin da dama, Kanal Dasuki din a maimakon hakan ma kusan a iya cewa shine ya jagoranci aiwatar da juyin mulkin shekarar 1983 da Shugaba Buharin ya ci gajiyar sa ya zama shugaban kasa a wancen lokacin.
Kunne-ya-girmi-kaka: Yadda aka sa Buhari cikin mari yayin juyin mulkin da aka yi masa a 1985
Kunne-ya-girmi-kaka: Yadda aka sa Buhari cikin mari yayin juyin mulkin da aka yi masa a 1985
Legit.ng Hausa ta tsinkayi Kanal Abdulmumini Aminu mai ritaya, wanda dan asalin Jihar Katsina ne, ya bayyana ko su waye Manjo-Manjo din guda uku da ya jagoranta wajen kamo Shugaba Buhari a 1985 lokacin da Janar Babangida yayi masa juyin mulki, a cikin wata tattaunawa da aka yi da shi a cikin jaridar ‘Sunday Trust,’ ta watan Agusta 2015.
Abdulmumini Aminu, ya ce, mutane uku ne wadanda shi da kansa ya jagorance su, suka je suka kamo Shugaban kasan na wancan lokacin, (Janar Muhammadu Buhari), sauran biyun sune, Lawan Gwadabe da kuma John Madaki.
Ya ce, “Tilas na bayar da shaidar ni na jagoranci kamo shi. Na ta fi Barikin Dodon Barrack a lokacin, tare da rakiyar Sojoji biyu, Manjo John Madaki da kuma Lawan Gwadabe. Mu uku ne muka je, amma a zahiri, ni na hau sama na kamo Buharin.
“Na kamo shi da cikakkiyar girmamawa, na sha karantawa a cikin kafafen yada labarai, mutane na cewa, wai mun ci mutuncin sa, mun wulakanta shi. Sam hakan ba gaskiya ne ba. Ni da Janar Buharin ne kadai muka san hakikanin abin da ya gudana a tsakaninmu a saman benen, ba wani abu makamancin hakan da ya faru.
“Mun ba shi duk girmamawar da ya kamace shi a matsayin sa na babba gare mu, domin ai ko kafin wannan lokacin, muna ba shi cikakkiyar girmamawa, saboda irin halin sa. Har kawo yau, muna ganin kimarsa, babu kuma wani munafunci a tsakanin mu da shi, shi kuma ya san matsayin bin umurni a aikin Soja, a lokacin da duk na gaba da kai ya sanya ka yin wani aiki