shirye shiryen zaben Najeriya, " anfara fafatawa tsakanin Buhari da Atiku - BESTAREWA BlOG

Header Ads

shirye shiryen zaben Najeriya, " anfara fafatawa tsakanin Buhari da Atiku

<
A ranar lahadi ne aka buga kugen  siyasa a Najeriya inda 'Yan takara
A matakin tarayya zasu soma yakin Neman zaben 2019
gadan-gadan.Dokokin hukumar zaben kasar, INEC, sun nuna
cewa 18 ga watan Nuwamba 2018 ita ce  ranar da a
hukumance za a soma yakin neman zaben.Mutum 78 ne ke
takarar shugaban Najeriya, sai dai masana na ganin fafatawar
za ta fi yin zafi ne tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari na
jam'iyyar APC da tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku
Abubakar na jam'iyyar PDP. Dukansu biyu shekarunsu na
haihuwa sun wuce 70.Shugaba Buhari ya ce zai nemi wa'adi
na biyu na shugabancin  kasar ne saboda "na kammala
ayyukan da na soma."Shugaban, wanda ya kayar da Shugaba
na wancan Goodluck Jonathan a zaben 2015, ya gina
takararsa ne kan abubuwa uku: wanzar da tsaro,  samar da
ayyuka da kyautata tattalin arzikin kasar, da kuma yakar
rashawaMasana harkokin tsaro  da dama irinsu Malam Kabiru
Adamu sun amince cewa shugaban ya samu gagarumar
nasara a fannin tsaro - musamman a yaki da kungiyar Boko
Haram wacce ta kashe dubban mutane sannan ta raba
miliyoyi daga gidajensu.


Wanda yai posting : h fashion

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.