Lafiya jari. Duniya sabuwa: Masana kimiyya sun sanar da gano maganin hana tsufa - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Lafiya jari. Duniya sabuwa: Masana kimiyya sun sanar da gano maganin hana tsufa

<
A bisa dukannanin alamu dai masana harkokin ilimin kimiyyar rayuwa ta dan adam na daf da kakkabe cutar 'tsufa' daga ban kasa sakamkon wani binciken da suka gudanar suka kuma samu zarafin gano wani ilimin da da ba'a sani ba a duniyar kimiyya.
Masanan dai dake a jami'ar Pittsburgh na Amurka sun yi nasarar gano wani sabon maganin da ake tunanin zai iya sabunta dukannin wasu kwayoyin halittar bil adama wadanda suka tsufa idan har akayi anfani da shi.
Duniya sabuwa: Masana kimiyya sun sanar da gano maganin hana tsufa
Duniya sabuwa: Masana kimiyya sun sanar da gano maganin hana tsufa
Legit.ng Hausa ta samu cewa sinadarin masanan sun sa masa suna ne da "Sinadirin Dauwamammiyar Kuruciya".
Da masanan suka yi bayani a mujallar raya fasaha da kimiyya ta MedicalXpress,tsufa ta samo asali ne daga raguwar wani sinadari mai suna "Klotho",wanda a yanzu haka suka yi nasarar gano hanyar bunkasa shi.
Sun dai tababatar da cewa,a duk lokacin da aka samu koma baya game da yawan wannan sinadirin,to za a dinka tsufa babu kakkautawa.
Ana kyautata zaton fara sayar da maganin nan da wani matsakaicin zamani.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.