Labaran siyasa :: Za mu ci gaba da binciken Ganduje —— Majalisar Kano - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran siyasa :: Za mu ci gaba da binciken Ganduje —— Majalisar Kano

<
A Najeriya, kwamitin majalisar dokokin jihar Kano da ya ke gudanar da bincike a kan zargin da ake yi wa gwamna Ganduje na karbar hancin miliyoyin dala, ya ce zai ci gaba da aikinsa, duk kuwa da umarnin da kotu ta bayar cewa ya saurara.
A jiya ne wata babbar kotun jihar Kano ta bukaci kwamitin da ya dakatar da binciken da ya ke yi bayan wata kungiyar lauyoyi masu rajin kare demokaradiyya ta shigar da kara tana zargin cewa kwamitin majalisar dokokin ba shi da hurumin binciken gwamnan.
Shugaban kwamitin Hon Bappa Babba Dan-Agundi, ya shaida wa BBC cewa, a fahimtar majalisarsu kwamitin zai ci gaba da gudanar da bincikensa kamar yadda ya tsara don ba cewa aka yi a daina aiki ba.
Me ya hana Ganduje zuwa majalisar Kano da kansa?
Majalisar jihar Kano za ta fara binciken bidiyon Ganduje
Majalisar Kano ta gayyaci Jafar Jafar kan bidiyon Ganduje
Bappa Babba Dan Agundi, ya ce kwamitin zai kuma je kotu domin ya girmamata saboda mutanen da ke amajalisar su ne yakamata su kare martaba da mutuncin kotun.
Shugaban kwamitin binciken ya ce, a abinda aka ba su, kotu ba ta ce su daina aikin da suke ba, amma kuma idan har suka je kotun ta kuma ce su daina binciken da suke yi, ai dole su girmama kotu.
Bappa Babba Dan Agundi, ya ce dangane da batun nazarin hotunan bidiyon tare da kwararru da za ayi kuwa, an samu ci gaba tun da an samu wadanda za su zo su bayar da shaida akai.
Dan majlisar dokokin ta jihar Kano, ya ce, dangane da batun ranar da za a kammala nazarin hotuna kuwa, dama a bisa ka'ida ranar Alhamis 8 ga watan Nuwamba yakamata a mika rahoton, don idan ba kotu ce ta tsaida da su ba, zasu iya kammala aikinsu sannan su mika rahoton.
Matashiya
A ranar Litinin ne biyar ga watan Nuwamba, wata babbar kotun jihar Kanon ta dakatar da majalisar dokokin jihar daga binciken da take yi a kan zargin da ake yi wa gwamna Abdullahi Umar Ganduje na karbar hanci.
Kotun ta bukaci kwamitin ya dakatar da binciken zuwa wani lokaci da za ta saurari karar da wata kungiyar lauyoyi ta gabatar mata.
Shugaban kungiyar Barrister Zubairu Muhammad ya yi zargin cewa majalisar dokokin jihar Kano ba ta da hurumin gudanar da bincike a kan Gwamna Ganduje kasancewar yana da rigar-kariya.
A cewar kungiyar, binciken da kwamitin ke yi tamkar cin zarafin kundin tsarin mulkin Najeriya ne.
A watan jiya ne majalisar dokokin ta kaddamar da kwamiti domin bincike kan bidiyon da ya nuna Gwamna Ganduje yana karbar miliyoyin dala daga wurin wasu 'yan kwangila.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.