Labaran siyasa :: El-Rufai ya yi kuskure da ya zabi Musulma mataimakiyarsa - Sheikh Gumi - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran siyasa :: El-Rufai ya yi kuskure da ya zabi Musulma mataimakiyarsa - Sheikh Gumi

<
Sanannen malamin nan na addinin Islama Sheikh Ahmad Gumi, ya soki shawarar da gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai ya yanke na daukar mace a matsayin mataimakiya a zabe mai zuwa.
Dr Gumi ya bayyana ra'ayinsa ne a yayin da gwamnan El-Rufai ya shaidawa wani taro na mabiya addinin kirista daga kudancin jihar Kaduna cewa babu batun addini ko kabilanci a zabin da yayi na musulma a matsayin mataimakiyarsa.
Kun san matar da za ta zama mataimakiyar El-Rufai?
Sulhunta Atiku da Obasanjo na je yi — Sheikh Gumi
Abin da na fada wa Atiku Abubakar a Kaduna – Dr Ahmad Gumi
Gwamnan na Kaduna ya zabi Dr Hadiza Balarabe a matsayin wadda za ta gaji Barnabas Bala Bantex wanda ke taimaka masa tun 2015.
Mista Bantex kirista ne kuma zai ajiye mukamin mataimakin gwamna ne saboda ya sami damar tsayawa takarar sanata.
Ku latsa hoton Sheikh da ke kasa don sauraron cikakkiyar hirarsa da Nurah Ringim kan batun:
Sheikh Gumi ya shaida wa BBC cewa bayanin da ya yi nasiha ce ga 'yan siyasa gaba daya, cewa dukkan abin da za su yi, su rika lura da lokacin da ake ciki da kuma halin da mutanen da suke shugabanta.
Ya kara da cewa a yanzu ba lokacin da ya kamata a yi la'akari da cancanta ba ne, kamata ya yi a yi la'akari da yanayin da ake ciki.
Dr. Gumi ya shan janyo ce-ce ku-ce a fagen siyasar Najeriya, musamman kan wasu kalamai da ya ke yi kan salon shugabancin Shugaba Buhari.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.