Labaran kannywood :: Rahama Sadau ta yi wa mai son auren ta fatan alheri - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran kannywood :: Rahama Sadau ta yi wa mai son auren ta fatan alheri

<
Fitacciyar jarumar Kannywood Rahama Sadau ta yi addu'a ga wani "masoyinta" wanda ya roki Allah ya ba shi matar kamarta.
Shi dai Khamisu S. Guyaba ya wallafa sako ne a shafin Twitter inda ya nuna matukar son da yake yi wa Rahama domin ya aure ta.
Sai dai ya kara da cewa idan hakan ba za ta yuwu ba yana so ya auri mai hali da ilimi da nutsuwa da kuma taimakon jama'a kamarta.
Masu bibiyarsa a shafin Twitter sun taya shi addu'a inda wasu ke cewa Allah ya cika masa burinsa yayin da wasu ke yi masa addu'ar zabi mafi alheri.
Daga bisani ne jarumar ta ba shi amsa inda ta roki Allah ya ba shi matar da ta fi ta sannan ta yi masa godiya.
Hirar Rahama Sadau da BBC Hausa kan ziyarar Priyanka a India
Hukumar tace fina-finai ta yafe wa Rahama Sadau
Ashe ba a dakatar da Rahama Sadau daga Kannywood ba?
"Allah ya ba ka wacce ta fi Rahama da komai. Na gode sosai," in ji jarumar.
Rahama Sadau ta dade tana jawo ce-ce-ku-ce a Kannywood ko da yake ta kwana biyu ba ta shiga bakin jama'a ba sakamakon karatun da ta tafi karowa a kasar Cyprus.
A shekarar 2016 aka kore ta daga shiga fina-finan Kannywood bayan an same ta da laifin "rungumar" wani mawaki Classiq a bidiyon wakar da suka fito tare.
Batun dai ya jawo zazzafar muhawara, ko da yake daga bisani an janye haramcin bayan da ta nemi gafara a wurin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.