Labaran duniya :: An rufe makaranta don dalibai sun fara sa hijabi - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran duniya :: An rufe makaranta don dalibai sun fara sa hijabi

<
Wani rikici ya kunno kai a makarantar sakandare mai zaman kanta ta Jami'ar Ibadan bayan tasa keyar dalibai zuwa gida.
Iyayen daliban sun yi zargin cewa hukumar gudanarwa makarantar sakandaren ta kulle makarantar tun bayan fara sanya hijabi da dalibai musulmai suka yi.
To amma kuma hukumar gudanarwar makarantar ta musanta batun rufe ta, illa dai ta ce ta haramta a shiga da hijabi a matsayin tufafin makaranta.
Tuni dai kungiyar kare hakkokin musulmai ta Muslim Rights Concern ta yi Allah wadai da wannan mataki da shugabannin makarantar suka dauka.
Yadda hijabi ya hana wata zama lauya a Nigeria
An yarda daliba ta sanya hijabi a wurin taron lauyoyi
Boko Haram: Shin za ku goyi bayan hana sa hijabi?
Ainihin abun da ya faru
Kulle makarantar sakandaren dai kamar yadda rahotanni suka nuna ya biyo bayan sanya hijabi da wasu dalibai suka fara, a wani bangare na suturta jikinsu kamar yadda addinin musulnci ya yi tanadi.
Makarantar sakandare ta jami'ar Ibadan da aka kafa sama da shekara 55 dai tana da tsarin tufafin makaranta da hukumomi suka amince a sanya.
Hukumar makarantar ta bayyana daukar mataki na hana daliban masu hijabi shiga makarantar domin kaucewar harzuka sauran dalibai, abun da zai iya zuwa da tashin hankali.
Tuni dai iyayen dalibai musulmai su ka yi Allah wadai da matakin da makarantar ta dauka.
Kungiyar tuntubar iyaye musulmai a sakon da ta aika ga shugaban makaranar sakandaren ta janyo hankalinsu cewa 'ya'yansu musulmai da ke daukar karatu a makarantar suna da hurumin amfani da da hijabi.
Kungiyar ta ce sanya hijabi wani bangare ne daga cikin sharuddan suturta jiki a addinance. Wani abu koma bayan haka ya tauye 'yancinsu na bil'adama.
Iyayen sun ce tun farko sun gabatar da wasika ga makarantar kan cewa 'ya'yansu musulmai za su fara sa hijabi daga zangon karatu na shekara ta 2018/19.
Wata malama da 'yarta ke karatu a makarantar ta ce: "Abin da ya faru ya fara tasiri ga daliban domin kuwa ba sa zuwa makaranta.
"'Yata tana karatu a makarantar, tana a ji uku - amma wannan krufewar ba ta shafi daliban da suke aji uku ba, saboda suna shirin rubuta jarrabawar WAEC.
Me hukumar makaranta ta ce?
To amma a cewar Mr. Femi Ogundaro shugaban gudanar da harkoki a makarantar ya ce ba a kulle makarantar ba.
Sai dai ya ce sanya hijabi ba ya cikin tsarin tufafin makarantar.
Ya ce: "Ina so na tabbatar muku cewa makarantar tana bude kuma akwai dalibai a ciki. Abin da muka sani shi ne cewa sanya hijabi ga daliban wannan makaranta ba ya cikin tsarin tufafi da hukumar gudanarwar makarantar ta amince da su.
"Ba za mu karya dokokin makarantar domin shigo da wani tsari da zai saba da yadda aka kafa makarantar tun farko ba.
"Muna sayar da tufafin makaranta, kuma in dalibai suka sa wani tufafi wanda makarantar ba ta amince to ba za a yarda a sanya su ba."
Ya kara da cewa a ranar Litinin ce wasu iyaye musulmi suka shigo makaranta suka raba hijabi ga dalibai - wani abu da ya saba da tsarin gudanawar makarantar.
Bincike ya tabbatar da cewa an kulle makarantar sai dai an bar makarantar a bude ga dalibai 'yan aji uku kadai da ke shirin rubuta jarrabawar karshe, inda rahotanni suka nuna sauran daliban an tasa keyarsu.
Hukumar makarantar ta ce iyaye musulmi da suke da 'ya'yansu a makarantar suna sane da dokokin makarantar wanda kuma suka amince da su tun kafin 'ya'yansu su fara daukar karatu.
Kungiyar kare hakkokin musulmi ta Muslims Rights Concern ta janyo hankalin makarantar mallakar jami'ar Ibadan cewa sanya hijabi ga musulmi fa ba kirkira ce tasu ba illa dai cika umarni ne da Allah ya ce a yi wanda kuma kundin tsarin mulkin Najeriya ya amince da 'yan cin musulmi amfani da hijabi.
Farfesa Ishaq Akintola ya fada wa BBC ta wayar tarho cewa ba za su yarda da cin kashi da ake yi wa musulmai 'yan makaranta a makarantun sakandare a kasar nan ba.
Ya ce: "Ba za mu amince da abin da makaranta ke cewa wai iyaye sun amince da tufafin makaranta amma ba hijab ba wanda da shi za a yi amfani da shi a makaranta. Ba za mu amince da wannan ba. Kuma za mu kalubalnci hakan.`"
Ya kara da cewa ko a kasashen da suka ci gaba kamar Burtaniya ko a Amurka ko a Sweden da wasu wurare suna bai wa dalibai mata musulmai damar amfani da hijabi duk da kayan makaranta da suke amfani da shi.
Wannan dai ba shi ne karon farko da dalibai musulmai suke fuskantar kalubale a makarantun sakandare ba.
Ko a Legas an sha tasa keyar dalibai musulmai komawa gida ko kuma a tilasta mu su cire hijabi kafin su shiga makaranta ko kuma azuzuwa.
A wasu lokuta kamar yadda kungiyar Musulmi ta MURIC ta nuna kan zo da duka da wahalshe da daliban.
Idan dai ana iya tunawa ko makarantar koyar da aikin lauyoyi ta kasa ta umarci wata daliba da ta kammala karatun digiri a kan aikin lauya tilasta ma ta cire hijabinta amma taki - wani lamari da ya haifar da rikici da ce-ce-ku ce.
An dai kafa makarantar sakandaren tun a shekarar 1963 da kuma take marabtar dalibai musulmi da kuma mabiya addinin Kirista.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.