Labaran Duniya :: Matan Saudiyya na zanga-zanga kan sanya abaya - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran Duniya :: Matan Saudiyya na zanga-zanga kan sanya abaya

<
Wasu daga cikin matan Saudiyya sun gudanar da zanga-zangar adawa da tilasta musu sanya abaya, wadda dogowar riga ce da ke rufe tun daga sama har kasa da suke sanyawa a lokacin da za su fita bayyanar jama'a.
Wannan bore dai na gudana ne a shafukan sada zumunta da muhawara, kuma sun sanyawa maudu'in suna ''sanya abaya a bai-bai'', tare da wallafa hotunan mata sanye da abaya da kuma nikabin rufe fuska wadda suke korafin tana takura musu.
A watan Maris da ya wuce, Yarima mai jiran gadon masarautar Saudiyya Muhammad bin Salman bin Abdul'azeez al-Su'ud ya bayyana cewa sanya doguwar abayar ba tilas ba ne ga matan kasar.
Kusan mutane 5,000 ne daga ciki da wajen kasar suka ta tsokaci kan batun a shafin Twitter.
ﺑﺎﻟﻤﻘﻠﻮﺏ ﺍﺣﺘﺠﺎﺟﺎ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻌﺎﺩﺍﺕ ﻭﺍﻧﻈﻤﺔ ﺍﻟﺪﻭﻟﺔ ﺍﻟﺘﻲ ﺟﻌﻠﺘﻨﺎ ﺗﺤﺖ ﺍﻟﺘﻬﺪﻳﺪ ﻟﻮ ﺗﺠﺮﺃﻧﺎ ﻭﺃﻇﻬﺮﻧﺎ ﻫﻮﻳﺎﺗﻨﺎ . ﻧﻀﻄﺮ ﻧﺸﺘﻐﻞ ﺩﻭﺍﻡ ﻛﺎﻣﻞ ﺑﺎﻟﻨﻘﺎﺏ ﻭﺍﻟﻌﺒﺎﻳﺔ ﺑﺤﺠﺔ ﺍﻥ ﺍﻟﻤﻜﺎﻥ ﻣﺨﺘﻠﻂ ﻭﻫﺬﺍ ﺍﻟﺤﻤﻞ ﺛﻘﻴﻞ ﺛﻘﻴﻞ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻜﺎﺋﻦ ﺍﻟﺒﺸﺮﻱ ﺃﻧﺎ . ﻟﺴﺖ . ﻣﻨﻘﺒﺔ . ﻳﺎﺑﺸﺮ ForcedToWearIt#
pic.twitter.com/OEsh0RZfNq
— #FreeSaudiActivists ﺣﻮﺭﺍﺀ (@Howwwra) 11 Nuwamba, 2018
As a #Saudi woman, I don’t enjoy freedom to cloth. I am forced by the law to wear Abaya (black robe) everywhere but my house, which. I. can’t. take. any. more.
# ﺍﻟﻌﺒﺎﻳﻪ _ ﺍﻟﻤﻘﻠﻮﺑﻪ
____
#BurnTheNiqab
#NoHijabDay
#MyStealthyFreedom#ForcedToWearIt#NiqabDoesNot
pic.twitter.com/ox51scXK3V
— ﻧِﻜّـﺎﻝ (@Nikkaal) 11 Nuwamba, 2018
# ﺍﻟﻌﺒﺎﻳﻪ _ ﺍﻟﻤﻘﻠﻮﺑﻪ
ﻣﺴﺘﻤﺘﻌﺔ ﺑﻨﻈﺮﺍﺕ ﺍﻟﺬﻫﻮﻝ pic.twitter.com/Y93GxlS5ZI
— Shafa (@Shafax6) 11 Nuwamba, 2018

Wace sutura matan Saudiyya za su sanya?
Gwamman shekaru da suka gabata, hukumomin Saudi na da tsaurin ra'ayi kan suturar da matan kasar ke sanyawa wadda za ta rufe baki dayan jikinsu a bainar jama'a, inda suke sanya abaya matukar musulmi ne.
Amma a watan Maris Yarima Muhammad ya ce mata ba sa bukatar sanya zumbuleliyar rigar, suna bukatar a dama da su a fagen suturar zamani matukar kayan ba sa nuna tsiraici don haka ba lallai sai sun sanya abaya ba.
A wata hira da gidan talabijin na CBS Yariman ya ce "dokokin addinin musulunci a bayyane suke, addinin ya amince mata su sanya tufafin da suka kaimuradi, abu mai muhimmanci shi ne dole su suturta jikinsu, kamar yadda aka umarci maza su aikata hakan."
Bin Salman ya kara da cewa, "Hakan ba yana nufin lallai sai sun sanya abaya ko bakin nikabin rufe fuska ba. Baki dayan zabi yana ga matan su zabi irin suturar da suke muradin sanyawa."
Me matan Saudiyya ke wallafawa a shafukan sada zumunta?
Wata mace mai suna Howra ta ce za ta fara sanya abaya a bai-bai domin nuna adawa da dokokin kasarta sannan idan har mata za su fita ba tare da abaya ba hakan na nufin babbar barazana ce gare su ta hanyar bayyanar da kansu ga jama'a.
Howra ta kara da cewa "Ya zama dole mu sanya abaya da nikabi a fuskarmu, saboda kullum abin da ake cewa shi ne muna aiki cakude da maza don haka dole ko ina a jikinmu ya rufu-ruf. Gaskiya wannan abun yana takura mana matuka."
Amma wata matashiya mai suna Shafa ta wallafa cewa ''ina jin dadin sanya abayata a bai-bai."
Shekarun baya da suka gabata dai matan Saudiyya sun fara sanya launuka daban-daban na abaya, ba kamar bakar abaya da kusan a iya cewa suka gada tun iyaye da kakanni ba.
Sannu a hankali suka fara sanya abaya mai budadden gaba da ana iya ganin suturar da suka sanya a ciki kamar wando, ko dogon siket da sauransu kamar yadda wani rahoton kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana.
A shekarar da ta gabata ne aka dage haramcin tuka mota da matan Saudiyya ke fama da shi, sai dai har yanzu yawancin matan da suka yi fafutukar tabbatar da hakan na garkame a gidajen kaso a kasar.
Tun daga wancan lokacin ake zargin yarima Muhammad da bada umarnin kashe dan jarida da ya yi kaurin suna wajen sukar yadda yake tafiyar da mulkinsa wato Jamalk Khashoggi a ofishin jakadancin kasar da ke birnin Santambul na kasar Turkiyya, amma Saudiyya ta musanta batun.
Wadanne abubuwa ne har yanzu matan Saudiyya ba za su iya aikatawa gaba-gadi ba?
Akwai abubuwa da dama da matan Saudiyya ba za su iya aikatawa gaba-gadi ba har sai tare da muharammansu, ko dai mahaifi, ko dan uwa, ko kuma mijin aure wasu lokutan ma har da Da.
Daga cikinsu akwai:
Neman izinin yin fasfo
Tafiya kasar waje
Aure
Bude asusun ajiya na banki
Kasuwanci
Yin tiyata yayin rashin lafiya
Barin gidan kaso
Batun muharrami kafin mata su gudanar da wasu harkokin rayuwa, ya taka muhimiyar rawa wajen kara wawakeken gibi da rashin daidaito tsakanin maza da mata a yankin gabas ta tsakiya.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.