Labaran Duniya :: Dalilin Dayasa ASUU za ta ci gaba da yajin aiki - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran Duniya :: Dalilin Dayasa ASUU za ta ci gaba da yajin aiki

<
Kungiyar malaman jami'a ta Najeriya, ASUU za ta ci gaba da yajin aikin sai baba-ta-gani da ta tsunduma tun a makon da ya gabata duk da koma teburin tattaunawa da gwamnati.
A ranar alhamis ne kungiyar ta koma teburin tattaunawa da gwamnatin Tarayya, amma bangarorin biyu sun amince su sake haduwa a tattauna a makon gobe inda ake sa ran zaman zai kunshi har da ministan ilimi.
A yayin da yake zantawa da manema labarai bayan tattaunawar da aka soma, Ministan kwadagon Najeriya, Chris Ngige wanda ya jagoranci wakilan gwamnati ya ce yana fatar tattaunawar da za a yi a gaba zai haifar da dakatar da yajin aikin.
Sai dai kuma a nata bangaren, kungiyar malaman ta ce sakamakon tattaunawar da za a yi nan gaba wanda ministan ilimi zai halarta shi zai tantance matakin da za ta dauka, ko ta janye yajin aikin ko kuma ta ci gaba sai baba-ta-gani.
Me ya sa kungiyar malaman jami'a ta shiga yajin aiki?
Minti 7 da Buhari: Abin da 'yan Najeriya ke son fada masa
Hakan dai na nufin daliban jami'o'in na Najeriya za su ci gaba da zama a gidajen iyayensu, inda kungiyar za ta ci gaba da yajin aikin har sai ta samu jituwa tsaakaninta da gwamnati.
A ranar 4 ga watan Nuwamba ne kungiyar ASUU ta shiga yajin aiki bayan kasa fahimtar juna tsakaninta da ministan ilimi Adamu Adamu kan bukatunta.
Kungiyar ta zargi gwamnatin Najeriya da gaza aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a baya game da yadda za a inganta yanayin aiki a jami'o'in, da kuma rashin biyan mambobinta kudaden alawus da wasu sauran bukatunta.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.