Labarin wasanni :: Gasar Zakarun Turai: Juventus ta doke Man Utd a gida - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labarin wasanni :: Gasar Zakarun Turai: Juventus ta doke Man Utd a gida

<
Kungiyar Juventus ta doke Manchester United da ci 1 - 0 a Old Trafford.
Kwallon da Paulo Dybala na kungiyar Juventus ya jefa a ragar Juventus kafin a tafi hutun rabin lokaci ce ta raba kungiyoyin biyu.
Haka aka buga wasan, wanda tsohon dan wasan United Cristiano Ronaldo ya buga wa kungiyar ta Juventus, wanda shi ne dawowarsa ta farko zuwa Old Trafford tun da ya koma kungiyar a bana.
United za su tafi birnin Turin domin karawa a karo na biyu da Juventus ranar 7 ga watan Nuwamba.
Yadda kungiyoyin suka shirya wa wasan
Dan wasan United na gaba Alexis Sanches ba zai buga wa kungiyarsa ba, saboda kocin United Jose Mourinho ya ce "Ba ya cikin ganiyarsa."
Amma Antonio Valencia, dan wasan bayan United zai iya samun damar buga wannan wasan a karon farko tun ranar 2 ga watan Oktoba bayan da aka yi masa tiyata a bakinsa.
Mourinho ya ce Valencia "Ya samu matsalar rashin lafiya - kuma an yi masa tiyata mai wahalaswa a bakinsa."
Ya kuma ce Valencia na bukatar lokaci domin ya warke: "Dalilin da ya sa bai yi atisaye na kwana 10 ba ke nan."
Kungiyar Juventus ta ce dan wasansu na gaba, Cristiano Ronaldo, wanda ya shafe shekaru shida a Old Trafford daga 2003 - 2009 na cikin wadanda za su buga wannan wasan.
Wannan ne karo na farko da dan wasan mai shekara 33 zai buga wasa a gasar Zakarun Turai tun da aka ba shi jan kati a wasan da Juventus ta buga da Valencia ranar 19 ga watan Satumba.
Amma 'yan wasan Juventus Mario Mandzukic da Emre Can da kuma Sami Khedira ba za su buga wannan wasan ba.
Jose Mourinho: Manchester United za ta farfado
An yi rikici da Mourinho bayan Chelsea ta farke ci na biyu
Cristiano Ronaldo ya musanta zargin yi wa wata mata fyade
Juventus

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.