Labaran yanma : Hanyoyi hudu da za a bi a magance rikicin Kaduna - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran yanma : Hanyoyi hudu da za a bi a magance rikicin Kaduna

<
Har yanzu al'ummar jihar Kaduna na karkashin dokar hana fita ta sa'o'i 24 bayan rikicin da ya faru a jihar.
A cikin wani jawabi da ya yi wa al'ummar jihar, Gwamna Malam Nasir El Rufa'i ya ce a ranar Talata ne kwamitin tsaron jihar zai gana domin diba yiyuwar sassautawa ko dage dokar.
A ranar Juma'a ne gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita ta sa'o'i 24 a garin Kaduna da Kasuwar magani da ke karamar hukumar Kajuru bayan barkewar rikici.
Kimanin mutum 55 ne 'yan sanda suka tabbatar da mutuwarsu sakamakon rikicin.
An dai an sha samun rikice-rikicen kabilanci da addini a jihar Kaduna kuma ba tare da an dauki matakai ba.
Masana na ganin akwai wasu dalilai da ke hana hukunta wadanda ake zargi da hannu a rikice-rikicen.
Abdul-Azeez Ahmed Abdulkadir wani dan jarida kuma mai sharhi kan sha'anin rikicin Kaduna ya bayyana wasu hanyoyi da yake ganin ya kamata abi domin shawo kan rikicin da ya ki ci ya ki cinye wa.
Alkalai
Ya ce ya kamata akwai wadatuwar alkalan da suka kamata a jihar Kaduna.
A cewarsa alkalan da Kaduna take da su ba su kai rabin abin da ake bukata ba domin hukunta masu laifi.
Rashin tattara shaidu
Haka kuma rashin tattara shaidu da hukumomin jihar ba su iya yi yana da wahala a iya gabatar da wani mai laifi a kotu, domin a cewarsa alkalai suna dogaro ne da shaidun da aka gabatar ma su.
"Rashin tattara shaidu daga bangaren Jami'an tsaro domin tabbatar wa alkali wanda ake tuhuma yana da laifi to babu yadda za a iya hukunta shi," in ji shi.
Gwamnati
Masanin na ganin rashin daukar matakin da ya kamata daga bangaren gwamnati na daya daga cikin dalilan da suka hana kawo karshen rikicin.
A cewarsa, Gwamna El Rufa'i ya sha fada cewa gwamnatocin da suka shude sun kasa daukar matakan da suka dace domin kawo karshen rikicin Kaduna.
Masanin na ganin ya kamata a ce El Rufa'i ya dauki matakan da yake nufi da ya kamata a dauka domin kawo karshen rikice-rikicen.
Siyasa
Masharhanta na ganin duk rikicin-rikicen da suka faru babu wani mutum daya da aka ce an hukunta ko an kai shi kotu.
Malam Kabiru Adamu, wani mai sharhi kan harkar tsaro a Najeriya yana ganin 'yan siyasa suna gudun sabawa kabilu da kuma addinan da ke jihar don gudun kada su juya masu baya a lokacin zabe.
Mutum 55 aka kashe a rikicin Kaduna – 'Yan sanda
Buhari ya yi Allah-wadai da rikicin Kaduna
Sai dai kuma a cikin jawabinsa, gwamna El Rufa'I ya ce ce za a hukunta mutane 25 da aka kama da ake zargi suna da hannu a rikicin da ya faru na kwanan nan da kuma mutum 63 da aka kama a rikicin da ya taba faruwa a watan Fabrairu a kasuwar magani.
Ya ce sai idan an fara ganin ana huhkunta mutanen da ke haddasa rikici da hasarar rayuka shi zai kawo karshen rikicin idan ba haka za a ci gaba da samun rikicin.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.