Labaran duniya :: mai ya haddasa. Rikichin Kaduna - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran duniya :: mai ya haddasa. Rikichin Kaduna

<
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da sabon rikicin da ya barke a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin kasar.
Ya ce bai ji dadin yadda rikici ya barke a jihar ba wanda kuma har ya haddasa rasa rayukan mutanen da ba su ji ba su gani ba har 55, kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter.
Shugaban Najeriyar, ya ce tuni aka umarci jami'an 'yan sanda da su yi duk abin da ya kamata wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a sassan jihar.
An dai tura dakarun kwantar da tarzoma na musamman zuwa jihar.
Har ila yau shugaban ya ce rashin mutunta rayuwar dan Adam, abu ne da ba za a amince da shi ba.
Ya ce "rikici ko tashin hankali abu ne marar kyau, don haka ina kira ga shugabannin al'umma da kuma 'yan kasa da ako da yaushe su rinka amfani da tattaunawa da hakuri da kuma juriya domin gujewa tashin hankalin da ka iya janyo babban rikici."
Daga nan ya yaba wa gwamnatin jihar Kaduna saboda matakan gaggawan da ta dauka bayan barkewar rikicin.
Shehu Sani: 'Na fice daga APC don gwamnoni sun fi karfin Buhari'
Gwamnatin Kaduna za ta bawa teloli kwangilar dinki
Ba talakawa ba ne a zuciyar el-Rufa'i - Shehu Sani
Gwamnatin jihar Kaduna dai ta sanya dokar hana fita ta daga safe zuwa dare wato tsawon sa'a 24 a cikin garin Kaduna da kewaye sakamakon rikicin.
A wani sakon Twitter da Gwamnan jihar Malam Nasir el-Rufai ya wallafa a shafinsa, ya ce an sa dokar ne ba tare da wani bata lokaci ba.
Kodayake bai bayyana dalilin daukar matakin ba, ya ce an yi hakan ne domin amfanin jihar, tare da shawartar jama'a su kiyaye dokar.
Wasu rahotanni da muka samu sun nuna cewa an samu tashin hankali a wasu yankuna na birnin na Kaduna, kamar su Marabar Rido da kuma wasu unguwanni a tsakiyar birnin.
A makon da ya wuce ne aka samu tashin hankali a garin Kasuwar Magani da ke yankin karamar hukumar Kajuru, lamarin da ya haifar da asarar rayuka fiye da 50 da kuma dukiya, wanda a kan hakan hukumomin jihar suka sanya dokar hana fita ta sa'a 24 a garin.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.