Labaran duniya ::: An kara sanya dokar hana zirga-zirga a Kaduna - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran duniya ::: An kara sanya dokar hana zirga-zirga a Kaduna

<
Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da sake sanya dokar hana zirga-zirga ta sa'o'i 24 a garin Kaduna da kewaye a ranar Juma'a.
Gwamnan jihar Nasir el-Rufa'i ne ya bayyana hakan ta shafinsa na Twitter.
Hakazalika ya ce dokar ta shafi garin Kasuwan Magani da Kajuru da Katari da kuma Kachia, kuma ta fara aiki ne daga karfe 11 na safiyar Juma'a.
Gwamnan ya ce an dauki matakin ne bayan kashe wani basarake HRH Agom Adara a ranar Juma'a wanda aka sace a makon jiya.
Daga nan ya bukaci al'ummar jihar da su kwantar da hankulansu,inda ya ba da tabbacin hukunta wadanda suka aikata hakan.
A ranar Laraba ne aka sassauta dokar hana zirga-zirga ta sa'o'i 24 a garin Kaduna zuwa sa'o'i 13.
Hanyoyi hudu da za a bi a magance rikicin Kaduna
Kalli hotunan wasu daga cikin wadanda rikicin Kaduna ya shafa
Jagoran awaren Biafra Nnamdi Kanu ya bayyana a Isra'ila
A ranar Litinin da dare ne gwaman ya sanar da mutanen jihar cewa mutum biyar ne suka rasa rayukansu a rikicin na baya-bayan nan a yayin wani jawabi da ya yi ta kafofin yada labarai.
Amma akwai rahotannin da ke cewa wadanda suka mutu sun kai mutum 26.
Hakazalika ya ce an kama mutane da adama da ake zargi da hannu wajen tayar da rikicin.
Ya kuma ce za a hukunta dukkan wadanda aka samu da laifin tayar da wannan hatsaniyar.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.