Labaran siyasa :: Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce babban abin da zai sa a gaba bayan komawarsa kasar daga hutu shi ne daure barayi. - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labaran siyasa :: Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce babban abin da zai sa a gaba bayan komawarsa kasar daga hutu shi ne daure barayi.

<
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce babban abin da zai sa a gaba bayan komawarsa kasar daga hutu shi ne daure barayi.
Shugaban ya bayyana haka ne a hirarsa da gidan talbijin na NTA jim kadan bayan ya isa fadar shugaban kasar da ke Abuja, babban birnin kasar.
Da aka tambaye shi game da abin da zai sa a gaba bayan ya yi hutun kwana goma, Shugaba Buhari ya ce "za mu daure barayi da dama wadanda suka jefa mu cikin matsin tattalin arziki. Da ma na san ana sa ran zan yi hakan, kuma zan yi."
Yaki da cin hanci da rashawa na cikin manyan abubuwan da Shugaba Buhari ya yi alkawarin aiwatarwa lokacin da yake yakin neman zabe.
Wadanne batutuwa Shugaba Buhari zai taras a Nigeria?
Hotunan komawar Shugaba Buhari gida daga Landan
Gwamnatin Shugaban na Najeriya ta gurfanar da manyan jami'an tsohuwar gwamnatin Goodluck Jonathan a gaban kuliya, inda ake zarginsu da sace kudaden gwamnati.
Sai dai jam'iyyun hamayya da wasu masu sharhi na zargin Shugaba Buhari da daure 'yan adawa kawai.
A cewar su, yawancin jami'an gwamnatinsa da 'yan jam'iyyar APC mai mulki na da hannu a zarge-zargen cin hanci amma ba a dauki matakin hukunta su ba.
'Yan kasar da dama na son Shugaba Buhari ya daure duk mutumin da aka samu da hannu wajen taba lalitar gwamnati ba tare da sani ko sabo ba.
Shugaban na Najeriya ya ayyana sha'awarsa ta sake tsayawa takara a zaben 2019, kuma masu sharhi na ganin kalaman nasa ka iya yin tasiri wurin sake zabensa.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.