Labarai duniya :: Sanata John McCain na Amurka ya mutu - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Labarai duniya :: Sanata John McCain na Amurka ya mutu

<
John McCain, wanda tsohon sojan Amurka ne wanda daga baya ya zama sanata, ya kuma tsaya takarar shugabancin Amurka ya mutu yana da shekara 81.
Mista McCain ya mutu ne a jiya Asabar kamar yadda wata sanarwa da ta fito daga ofishinsa ta bayyana.
Iyalan gidansa na tare da shi a lokacin da ya cika.
Likitoci sun gano cewa yana da wani tsiro a cikin kwakwalwarsa tun a watan Yulin 2017, kuma tun wancan lokacin yake karbar magani.
Iyalansa sun bayyana cewa ya yanke shawarar daina shan maganin ne a ranar Jumma'a, kuma rabonsa da zuwa aiki a birnin Washington tun watan Disambar bara

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.