Siyasa :: Shugaba Buhari ya gana da Kwankwaso - BESTAREWA BlOG

Header Ads

Siyasa :: Shugaba Buhari ya gana da Kwankwaso

<
Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Abubakar Badaru, da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da kuma shugaban jam'iyyar APC Adams Oshiomole a fadar shugaban kasa.
Rahotanni sun ce ganawar da suka yi a ranar Litinin, wani yunkuri ne na dinke barakar da ke tsakanin 'ya'yan jam'iyyar APC.
An yi amannar cewa sanatan da ke wakiltar jihar Kano a Majalisar dattawan kasar na shirin ficewa daga jam'iyyar APC mai mulki tare da magoya bayansa.
Shin Kwankwaso zai iya doke Buhari a zaben 2019?
Kwankwaso ko mazabarsa ba zai iya kawo wa ba — Ganduje
Zan iya kayar da Buhari idan PDP ta tsayar da ni — Kwankwaso
Hakan ya biyo bayan sabanin da sanatan ya samu da gwamnan jihar Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje.
Sanatan da magoya bayansa ba su halarci babban taron jam'iyyar APC da aka yi a kwanakin baya ba.
Wata alama da ta kara nuna cewa sanatan da magoya bayansa na shirin ficewa daga jam'iyyar ta APC.
Sai dai za a iya cewa babu tabbas ko ganawar za ta sa tsohon gwamnan ya sauya shawarar da yake yi ta ficewa daga jam'iyyar APC din.

No comments

Theme images by friztin. Powered by Blogger.